Yadda Aka Gano Likitocin Bogi 20 A Wani Asibitin Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau

Shugaban ma’aikatan jihar Zamfara Ahmad Liman, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tantancewa, tare da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Duba Saba’in ya bayyana cewa kwamitinsa ya gano ma’aikatan bogi da dama a cikin jadawalin albashin Zamfara, wanda suka haɗa da Likitocin bogi 20 a wani asibiti a jihar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirin gwamnatin Zamfara na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na 70,000.

Gwamnati ta kafa kwamitoci da za su tantance haƙiƙanin adadin ma’aikatan jihar da kuma bayar da shawarwari kan sabon tsarin albashin.

Daga nan Ahmad Liman ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar Zamfara na aiwatar da cikakken tsarin mafi ƙarancin albashi da zarar kwamitin ya miƙa rahotonsa a ƙarshen watan nan.

Ya ci gaba da cewa kwamitin na aiki tuƙuru don ganin an yi cikakken aiki da nufin tsaftace alƙaluman lissafin albashin jihar domin aiwatar da albashi yadda ya kamata.

Ya ce, “Kuma Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne, ana yi wa wasu ma’aikatan aringizon albashi, wasu kuma suna amsar albashi biyu a cikin Jihar.”

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?