
Daga Hadi Bawa
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ba da umarnin janye dukkan jami’an tsaron da ke gadin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
A ranar Alhamis ne hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa (EFCC) ta bayyana Bello, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin almundahanar Naira biliyan 80.
Fitaccen Lauyan nan da ke Legas, Femi Falana (SAN) ya yi watsi da ikirarin da tsohon gwamnan ya yi na cewa ba za a iya kama shi ba saboda umarnin da wata babbar kotun jihar Kogi ta bayar.
Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun ya ba da umarnin janye dukkan jami’an ‘yan sandan da ke da alaka da tsohon gwamnan ta hanyar sakon da ya aika wa jami’ansa.
Takardar mai lamba: “CB:4001/DOPS/PMF/FHQ/ABJ/VOL.48/34 ta ce: “IG ya ba da umarnin janye dukkan ‘yan sandan da ke da alaka da mai girma tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.
“Ku yi aiki da wannan umarnin, kuma ku kula da shi don hakan Yana da matuƙar mahimmanci,” in ji shi.
Ita Hukumar shige da fice ta kasa (NIS) a ranar Alhamis din da ta gabata ta sanya Bello a cikin jerin sunayen mutanen da ke sanya wa ido, abin da zai sa a hana shi kasashen ketare.
NIS ta ce; “Sun yi haka ne saboda Bello na fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya Abuja” kan badakalar kudaden haram da sauran laifuka.
Takardar, wacce aka rabawa Daraktocin Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) da Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA) da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, ta bukaci hukumomin tsaro su kama Bello a duk inda ya suka gan shi a fadin kasar nan.
Babban Lauyan Tarayya Lateef Fagbemi ya bukaci Bello da ya mika kansa girma da arziki.
Ba a dai san inda yake ba har yanzu, yayin da gwamnatin Jihar Kogo ta musanta zargin da ake yi wa gwamna Usman Ododo da cewa shi ya boye shi.
EFCC ta yi barazanar neman taimakon sojoji domin cafke tsohon gwamnan idan ya ci gaba da kin bin doka da oda.
Da yake mayar da martani a kan ikirarin da Bello ya yi cewa EFCC ta ki bin umarnin babbar kotun jihar Kogi ta neman kama shi tare da gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, Falana ya ce ikirarin ba shi da tushe ko kadan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta bi umarnin babbar kotun jihar Kogi ta hanyar gurfanar da Bello bisa zargin almundahanar kudi sama da N80bn.
Ya bayyana umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar na kama Bello domin gurfanar da shi a matsayin wanda ya yi daidai da umarnin babbar kotun jihar Kogi.






