DAGA MUKHTAR YAKUBU
Idan Allah ya kaimu gobe Alhamis 10 ga Yuli za a yi taron tantance Jaruman da za fito a sabon ɗin Ƙwaryar sama wanda za a fara ɗauka nan da ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
Fim ɗin wanda fitaccen Furodusa Zahraddin Jalabi ya ɗauki nauyin shiryawa, kuma Furodusa Usman Ahmad Usee zai kasance mai kula da shirin. Sai kuma Yunusa Mu’azu da Nura Mai Shabbabu Mubarak za su kasance masu bayar da umarni. Sai kuma marubuci Aminu Idris Abdullahi.
Taron tantancewar na maza da mata zai kasance a tun daga misalin ƙarfe 10 na safe har zuwa yamma a harabar gidan talbijin na Abubakar Rimi ARTV da ke titin Maiduguri a Unguwar Hotoro da ke cikin garin Kano. Ana sa ran za a samu halartar manyan baƙi kamar Shugaban Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano Abba El-Mustapha, Shugaban Ƙungiyar Arewa Film Mekars, ƙungiyar Jarumai da na MOPPAN.
Don haka Furodusa Zahraddin Jalabi yake gayyatar dukkan masu sha’awar shiga cikin fim ɗin ko kallon yadda tantancewar za ta kasance da su halarci wajen taron da misali ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis ɗin domin shiga cikin tantancewar ko kallon yadda za ta kasance.






