Za Mu Ba Sabon Kwamishinan Ruwa Haɗin Kai Don Cimma Nasara – Injiniya Abdulrazaƙ

Daga Ibrahim Muhammad

Sabon kwamishinan ma’aikatar ruwa na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya ce a za su yi duk abin da ya kamata don ganin gwamnatin Kano ta sauke alƙawarin da ta ɗauka a kan kyautata ci gaban al’ummar Kano .

Ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar al’ummar masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Doguwa suka yi masa rakiya yake karɓar aiki daga tsohon kwamishinan ma’aikatar ruwa da aka mayar ma’aikatar ilimi Gwani Ali Bukar Makoda a ma’aikatar ruwa ranar Talata.

Ya ce daga abin da yake alfahari da shi a matsayin da ya yi na kwamishinan ilimi shi ne yadda ya yi aiki tuƙuru.

Mutane daga gida da sassan duniya suka amince Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki layin gyaran ilimi suke ta ba shi lambobin yabo a kan ilimi haka yake so su yi irin wannan aiki a ma’aikatar ruwa da ya dawo dan ganin an ɗora Kano a kan samun ruwan sha.

Hon. Haruna Doguwa ya ce yana jin daɗi da a cikin ‘yan shekarunsa ya yi Kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kano ba don ya fi kowa ba, Allah ne ya so ya yi masa hakan, yana kuma yi wa godiya ga Allah da wannan dama da ya ke ba shi.

Ya yaba da irin ƙoƙari da Kwamishina da ya gada, Gwani Ali Haruna Makoɗa ya yi na samar da ruwan sha ga al’ummar Kano. Sannan ya yi kira ga mutanen Kano su ƙara haƙuri gwamnati na aiki domin kawo ƙarshen matsalar ruwa. “Akwai injuna da aka yi oda za su zo da za a yi amfani da su wajen samar da ruwa da abubuwa da ake ta yi na samar da ruwa a jihar Kano,” in ji shi.

Hon Doguwa ya ce, “Mai girma Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da gaske yake, kuma cikin yardar Allah za mu yi aiki tuƙuru wajen samar da ruwa a Kano,” ya tabbatar.

Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida bayan tarɓar, sabon Kwamishina na ma’aikatar ruwa, babban sakatare na ma’aikatar, Injiniya Abdulrazak Haruna ya bayyana cewa Gwani Ali Haruna Makoɗa tsohon Kwamishinan ma’aikatar shugaba ne na gari mai dattaku, duk da bai daɗe da zama da shi ba, amma ya same shi mai ƙudiri mai kyau ga al’ummar Kano. Ya ba da kyakkyawan gudunmuwar yin aiki a ma’aikatar ruwa suna fata inda ya koma ya dora yanda ilimi zai ci gaba da haɓaka.

Babban sakataren na ma’aikatar ruwan na jihar Kano ya ce suna yi wa sabon Kwamishinan da aka kawo Hon. Haruna Doguwa albishir da cewa zai sami ma’aikata masu ƙwazo da za su ba shi cikakken haɗin kai da goyon baya domin kai wa ga nasara kamar yadda aka bai wa tsohon Kwamishina.

Injiniya Abdulrazak Haruna ya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf mutum ne mai son ci gaban jihar Kano, “Domin duk abin da ya shafi ma’aikatar ruwa idan aka kai masa nan da nan yake ba da amincewa aje a gudanar. Muna fata Allah ya ci gaba da riƙo da hannunsa da dukkan masu aiki da shi,” ya yi addu’a.

Shi ma shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Doguwa, Auwalu Doguwa da yake cikin tawagar da suka rako Kwamishinan ya gode wa Gwamna Abba Kabir bisa aiki da yake da Haruna Doguwa suna alfahari da irin muƙamai da yake yi na Kwamishina a ma’aikatu uku tun daga na ilimi mai zurfi, ya dawo ya yi na ilimi yanzu aka dawo da shi na ruwa, suna alfahari da abin da ya yi na jagorantar kai ɗalibai ƙasashen duniya lokacin Kwankwaso, kuma ya dawo a wannan gwamnati ya ba da gudunmuwa wajen gyara ilimi. “Muna fata zai yi aiki tuƙuru a ma’aikatar ruwa da aka dawo da shi don ya wadata jihar Kano da ruwa.”

  • Related Posts

    Bincike Ya Tabbatar Ƙungiyar Da Ta Zargi Gwamna Lawal Da Yi Wa ’Yan Bindiga Afuwa Ta Bogi Ce

    An gano cewa zargin da ake yaɗawa cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi afuwa tare da sakin ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci ba shi da tushe…

    Gidauniyar Abba Aliyu Gandu Ta Raba Solar Ga Al’umma

    Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal