Daga Ibrahim Muhammad
Alhaji Balarabe Rufa’i, ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen 2023 a jam’iyyar ADC, kuma jigo a ƙunshin shugabancin jam’iyyar na ƙasa, ya bayyana taron da suka yi a Kano da cewa na ƙoƙarin haɗa kan jam’iyyu ne domin a tunkari jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027 don kawar da ita.
Ya ce taro ne na haɗuwa da jam’iiyyu ba tare da nuna wata ta fi wata ba, ko wata ba ta kai wata ba, haɗa kai za su yi gaba ɗaya domin kowa ya san irin halin da ake ciki a wannan ƙasa babu tsaro, mutane ba sa iya ciyar da kansu, ma’aikata ba sa iya zuwa aiki, ƙasa tana cikin halin rashin tabbas.
Ya ce shi kuma shugaban ƙasa ya yunƙura kowa sai ya dawo jam’iyyarsa ta APC ta tsoratarwa da bai wa wasu kuɗi, shi ya sa jiga-jigan siyasa na wannan ƙasa wanda suke da kishin ƙasa suka ga ba zai yiwu a bar dimakraɗiyya ta koma hannun mutum ɗaya ba, shi ne aka ce a zo a haɗa kai wuri guda a tunkari APC don a bai wa al’umma dama su yi zaɓe.
Ya yi nuni da cewa abin da ake kai yanzu shi ne, yawancin jam’iyyun sai ka ga mutum yana PDP, amma sai a ba shi Minista a APC yana yi wa APC aiki, sai mutum yana LP sai a ba shi muƙami yana yi wa APC aiki. “Wannan ya nuna yanzu babu jam’iyyun adawa, shi ya sa ake da buƙatar a zo a yi wannan haɗin kai a fitar da jam’iyyar da za ta tunkari jam’iyya mai mulki. Muna fata za a yi wannan abu cikin kwanciyar hankali domin a samar da zaman lafiya da cigaban al’umma,” inji shi.
Honarabul Balarabe Rufa’i ya ce ƙofarsu a buɗe take kowa ya zo. “Kuma ba wani da zai kawo mana cikas, harka ce ta magana ta talakawa sun gaji da tsarin da ake musu mulki suna nema su bijire. Kashi 80 zuwa 90 na ‘yan ƙasar nan sun gaji da wannan tsarin da ake kai saboda ba sa iya cin abinci da kai ‘ya’yansu makaranta da kula da lafiyarsu. Dan haka tafiyarmu ta fi ƙarfin wani ya zo ya ɓata ta,” ya jaddada.
Alhaji. Balarabe Rufa’i ya ce yanzu mutane kansu a waye yake, shekaru biyu da gwamnatin Tinubu take ciki ana cikin yanayi na tsananin wahala da halin ƙaƙa-ni- ka-yi, su kuma jam’iyyun hamayya ana bai wa wasu a cikinsu suna haifar da rigama. “Haka aka dasa rigama a cikin LP da kuma cikin PDP. Shi ya sa ake so a haɗe waje guda da za a zo a ceto al’ummar ƙasar nan,” ya bayyana.








