Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa aure tsakanin Ango da Amarya ana yin sa ne a bisa soyayya, yarda da gamsuwa tsakaninsu, za su zauna tare kamar yadda Allah ya haɗa su da kyakkyawan burin cimma manufa ta alheri a rayuwarsu.
Jagoran Kwankwasiyya na ƙaramar hukumar Doguwa, kuma mai bai wa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf shawara a kan tsare- tsaren siyasa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Doguwa a karo biyu, Hon. Ali Abdu Doguwa ne ya bayyana hakan a ɗaurin auren ɗan Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Gwani Ali Bukar Makoɗa.
Ya ce zaman aure sai an yi haƙuri a tsakani, domin daga aure ne ake gina wata al’umma da Allah ne ya san ‘ya’ya da za su haifa a rayuwa da alherin da zai biyo baya a rayuwar Ango da Amarya.
Hon. Ali Abdu Doguwa, wanda tsohon Kwamishina ne na dindindin a jihar Kano, kuma tsohon mai bai wa tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Olufemi Hakeem Gbajabiamila CFR shawara ya ce, uban Ango da aka ɗaura wa aure Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Gwani Ali Bukar Makoɗa yayansu ne, kuma mai gidansu, mutumin arziƙi ne da hakan tasa ɗimbin al’umma suka zo suka shaidi ɗaurin auren ɗansa da taya shi fatan alheri.
Hon. Ali Abdu Doguwa ya ce, a matsayinsa na Jagoran Kwankwasiyya na ƙaramar hukumar Doguwa, wanda jagoransu na Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ɗora shi, ya ba shi amana ne don kawo gyara a tsarin Kwankwasiyya a Doguwa, kuma suna aiki tuƙuru don cimma nasara.








