Al’ummar Musulmi sun fito zanga-zangar lumana don nuna ɓacin ransu bisa kalami da suke zargin Shaikh Lawan Abubakar, Limamin masallacin Triumph, ya yi kan Annabi Muhammadu (SAW).
Masu zanga-zangar sun je gidan gwamnatin jihar Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbe su, tare da yi musu jawabi.
Abin da ya jawo yin zanga-zanga shi ne ɓullar ne wani bidiyo da aka ji Shaikh Lawan Triumph na musanta cewa haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da kaciya wani al’ajabi ne, yana mai cewa ruwayoyin da suka kawo haka ba su da inganci.
Da yake magana da masu zanga-zangar, Gwamna Abba ya roƙe su da su kwantar da hankali, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki matakin da bai saɓa wa shari’a ba.
Ya kuma buƙace su su gabatar da takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.
Masu zanga-zangar sun amince da wannan umarni, inda suka tsara kai takardar da gwamnan ya nema da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis.
Gwamna Abba ya ce, gwamnati za ta yi duba a kan buƙatar masu zanga-zangar.






