Ƙungiyar ‘Yan Tifa Ta Nemi Gwamnatin Jihar Kano Ta Samar Musu Motoci Da Za Su Riƙa Biya Cikin Sauƙi

Daga Ibrahim Muhammad

Haɗaɗdiyar ƙungiyar ‘yan Tifa da dangoginta na ƙasa reshen jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta taimaka wa ‘yan ƙungiyar ta ba su motocin tifa bashi a cikin sauƙin kuɗin da za su riƙa biya a hankali hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkokinsu da sakawa matasa aiki.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Shafi’i Zainawa ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen taron ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Ya yi nuni da cewa idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin Abba take abubuwa na hangen nesa suna kira a tsaya su ma a dubi lamarinsu a sama musu motoci a matsayin na bashi yadda ake bai wa ƙungiyoyi na ‘yan kasuwa a ɗora su a kan layin da za su riƙa biya a hankali cikin sauƙi.

Da ya juya kan ranar ma’aikata ta duniya da ake ya ce abin alfahari ne gare su sun kuma gamsu da yadda aka gudanar da taron na bana a kan lokaci aka yi aka gama.

Ya ce su a tsarin aikinsu a halin da ake ciki yanzu suna tafiya ne da yanayi da ake ciki na tsadar rayuwa suna ta ƙoƙari su ma su ga sun sayar da kayan su cikin sauƙi yadda masu ƙaramin ƙarfi za su yi amfani da kayan wajen gine-gine.

Ya ce suna alfahari da cewa masu sana’ar tifa mutum ne da shi ɗaya yana samar wa mutane da yawa aikin yi a yau ɗin nan idan tifa ta tsaya dabbar da take cikin gida a daure sai ta san ta tsaya.

Ya ce, “Yanzu muna fuskantar ƙalubale iri-iri musamman tsadar rayuwa, abin da ka saba sayen sa N10,000 na kayan gyara a baya a yau in ka riƙe N50,000 ba za ta saya maka wannan abin ba. Ba domin ƙalubale da ake fuskanta na tsadar kayan gyara a sana’ar tifa ba da an sami sassauci wajen kayan gine-gine a birane da ƙauyuka.”

Kwamared Ibrahim Shafi’i Zainawa ya ce, suna da mutuƙar buƙatar neman tallafin gwamnatin jihar Kano domin a irin aikace aikacensu suna daga waɗanda ke samar da aikin yi a tsakanin matasa a jihar suke kuma yin sharar kwarurruka wanda ya kamata ma a ce gwamnati na ba su wasu abubuwa na kulawa na musamman domin ƙoƙarin da suke wajen hana zaizayar ƙasa da ambaliyar ruwa, domin duk wurare da suke ɗaukar kayan aikinsu suna share shi yadda idan ruwa ya zo ba za a sami ambaliyar ba.

Ya ƙara da cewa a harkar kwashe shara da ake a jihar Kano a wurin mai tifa ba ƙaramin abin alfahari ba ne don sharar ce ke toshe waɗansu magudanan ruwa da ke haifar da ambaliyar ruwa.

Kwamared Ibrahim Shafi’i Zainawa ya nemi gwamnati ta kula ta sa ido a kan harkar tifa don ba su gudummawa da ta dace, musamman akwai wani gwanjon motoci da aka yi musu a gwamnatin da ta wuce aka ɗan sami matsaloli duk da ana ta bibiyar abin gwamnati tana iya ƙoƙarinta wajen yin bincike da ƙoƙarin samar da maslahar al’umma a kan motocin.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe