Daga Ibrahim Muhammad
Ƙungiyar kasuwar Galadima ta fara aikin sabunta babbar gadar shiga kasuwar da ta rushe sakamakon yawan manyan motocin da ke shiga da fita kullum.
Shugaban kasuwar, Alhaji Mustapha Shuaibu Sulaiman, ya ce ganin cunkoson ayyukan gwamnati, ƙungiyar kasuwar ta ɗauki nauyin aikin, wanda ya haɗa da fashe gadar gaba ɗaya, kwashe ta da sayen katakwaye, fulawus, rodika da sauran kayan aiki.
Ya ce aikin zai ci kusan N700,000, kuma ana gudanar da shi ne da kuɗaɗen da ‘yan kasuwa ke bayarwa da kudin shiga motocin kaya.
Mustapha ya ce bayan aikin gadar, ana faɗaɗa ofishin ‘yan sanda da ke cikin kasuwar domin ƙarin tsaro, tare da gina bene da zai zama ofishin gudanarwa, yayin da ƙasa za ta zama ɗakin ajiye masu laifi kafin safiya.
Ya kuma ce kasuwar ta samar da ofishin Civil Defence, ta sanya fitilu masu amfani da hasken rana da gyaran magudanan ruwa, duk a ƙoƙarin inganta tsaro da tsabtace muhalli.







