Daga Ibrahim Muhammad
Ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala da za su tafi karatu manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan da gwamnatiin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun gudanar da taron godiya ga Jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da sauran muƙarraban gwamnati ‘yan asalin Dala bisa wannan dama da aka ba su.
Taron da aka gudanar da shi a ɗakin taro na Ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano a yammacin ranar Lahadi ya sami halartar masu ruwa da tsaki a tafiyar Kwankwasiyya na Dala da suka haɗa da jagoran Kwankwasiyya na ƙaramar hukumar Dala Alhaji Ɗayyabu Ahmed Maiturare da shugaban ƙaramar hukumar Hon. Surajo Imam, wanda mataimakinsa Hon. Abdul’azez ya wakilta da kwamishinoni da sauran ‘yan jam’iyyar NNPP.
A jawabinsa a yayin taron, Jagoran Kwankwasiyya, shugaban jam’iyyar NNPP na Dala, Alhaji Ɗayyabu Ahmad Maiturare Galadiman Gado Da Masun Kano, ya nuna farin ciki bisa taron da ɗaliban ‘yan asalin Dala da za su je ƙaro karatu suka shirya suka kira su a matsayin su na iyaye da abokan arziƙi suka taya murna suka yi godiya a kai.
Ya ce su al’ummar Dala babu abin da za su ce da Gwamnan jihar Kano sai fatan alheri da addu’ar Allah ya cigaba da riƙo da hannunsa ya biya buƙatarsa yadda ya faranta wa al’ummar Dala da ‘ya’yansu shi ma Allah ya faranta masa.
Ya yi nuni da cewa sun san ana kula da al’ummar Dala a wannan gwamnatin, an ba su dama an ɗauki ma’aikata manya da ƙanana an ba su muƙaman Kwamishinoni da dama kuma ga aikace-aikace da ake yi da ya shafi al’umma na tituna, makarantu da bayar da cikakken dama ga shugaban ƙaramar hukumar Dala ana aikace-aikace.
Alhaji Ɗayyabu Ahmad Maiturare ya ce duk waɗannan abubuwa da ake musu bai sani ba ko gwamnati tana la’akari ne da yawan da suke da shi ne na al’umma ne ko kuma irin yawan gudunmuwa da suke bayarwa ne a harkar siyasa na tabbatar da nasarar tsarin Kwankwasiyya shi ya sa ake musu wannan tagomashi, amma dai ƙaramar hukumar Dala kome aka yi mata ta cancanta suna godiya a kai da neman kari.
Shi ma a nasa jawabin Kwamishina Tsaro na cikin gida na jihar Kano AVM Ibrahim Umar mai ritaya ya yi kira ne ga ɗaliban ‘yan asalin Dala da gwamnati da ɗauki nauyinsu cikin waɗanda za su qaro karatu a manyan jami’o’i daban-daban a ciki da wajen ƙamkasar nan su zama jakadu nagari ga ƙaramar hukumar da jihar Kano, kuma su sani cewa ilimi ne tushe ne da zai kai su duk wani mataki na cigaba da ba su za ta ba.
Ya ƙara da yin nasiha gare su da cewa duk inda suka sami kansu su ɗauki kyakkyawan al’adu na zamantakewa na wajen, su guji duk wani abu mara amfani, su zama masu kiyaye mutuncinsu da na addininsu da kuma al’adarsu.
Ya yaba irin kyakkyawan tunani na Jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na fito da tsarin ɗaukar nauyin yara ana tura su karatu manyan jami’o’i domin yin karatun digiri na biyu domin bunƙasa cigaban al’ummar jihar Kano..
A nasa jawabin shugaban ɗalibai ‘yan asalin Dala da gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin karatunsu a jami’o’i daban-daban Dakta Umar Hadi Tijjani ya gode wa Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan manyan makarantu, mataimakin Gwamnan jihar Kano Aminu Abdussalam Gwarzo da wannan dama da aka ba su da za su je karatu wasu a ƙasar Indiya, wasu a manyan jami’o’i na wasu ƙasashen wasu a cikin ƙasa.
Ya ce ɗaliban da za su karatun kashi na biyu ne daga cikin su 1001 da aka ɗauka. Akwai waɗanda za su ƙasashen waje su 350 da wanda za su yi karatu a cikin ƙasar nan da jimlar su ya kai 650 ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala guda 54 ne a ciki.
Dakta Umar Hadi Tijjani ya ce maƙasudin yin taron na godiya ne ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da dukkan masu ruwa da tsaki da sukayi tsayin daka aka sami nasarar tura su karatun, sun haɗa iyaye da shugabanni ne su saurari shawarwarinsu da yin godiya ga irin tallafin da aka ba su na harkokin karatun su.
Ya ce daga cikin tallafi da aka ba su akwai na kwamfutoci guda 51 wanda Kwamishinan Tsaro na cikin gida Ibrahim Umaru ya ba su 20 daga ciki shi ma Kwamishinan Muhalli Dakta Ɗahiru Hashim ya ba su 20 ita ma a ƙaramar hukumar Dala ta ba su 10, sannan shugaban (ACReSAL) Hon. Amin Giɗaɗo Yusha’u ya ba su guda huɗu, Kwamishinan Ma’aikatar Ƴaɗa Labarai Ibrahim Waiya ya ba su tallafi kuɗi N1,000,000 .
Dakta Umar Hadi Tijjani shugaban ƙungiyar ɗalibai ‘yan Dala da za su tafi karatu ƙasar Indiya ya ce fatansu ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta maimaita a yi ta tafiya a kan tsarin jagoranci na Kwankwasiyya da ake don ɗan talaka da bai san kowa ba ya cigaba da samun dama kamar yadda su ma ba wanda suka sani gani suka yi kawai sunayensu ya fito bisa cancanta za a tura su karatun.
Taron ya sami halartar wakilan iyayen yara da mayan shaihunan malaman jami’a ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala.








