Ɗaurin Auren ‘Ya’yan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano: Karamcin Mahaifinmu Ya Sa Ɗimbin Al’umma Suka Halarta -Mujahid Aminu Abdussalam

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana zaman aure tsakanin ma’aurata da cewa abu ne da sai an yi haƙuri da juna, kuma zama ne na zo mu zauna, zo mu saɓa da Hausawa ke cewa Allah ya saɓa hali da haƙuri ne zai jagoranci a kai.

Mujahid Aminu Abdussalam daga mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a lokacin walimar ɗaurin auren ƙannensa a ranar Lahadi.

Ya ƙara da cewa shi aure muhimmin ibada ne idan ma’aurata suka ɗauka zaman ibada suke sai abubuwa su tafi yadda ya kamata, domin duk soyayya daga waje ake gina ta idan aka ɗaura aure aka zo aka zauna shi ne halaye ke fitowa na zahiri na miji da mata dole sai an fahimci juna an yi haƙuri a zamantakewa.

Mujahid Aminu Abdussalam ya ce ba abin da za su ce wa mutane sai Allah ya saka da alkhairi, an zo daga wurare daban-daban don taya su murna.

Ya ce irin wannan taro ya nuna irin kyakkyawar mu’amala da mahaifinsu ke da ita da mutane irin wannan mu’amala da mutuntaka ita ta sa ɗimbin mutane suka zo daga ko’ina.

Mujahid Aminu Abdussalam ya ƙara yin addu’a da fatan waɗanda aka ɗaura wa auren Allah ya ba su zaman lafiya.

A safiyar ranar Lahadi ne dai Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da madugin Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da sauran al’umma daga ciki da wajen jihar Kano suka halarci ɗaurin auren ‘ya’yan mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam guda biyu da aka gudanar a masallacin Juma’a na Alfurƙan.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe