Daga Ibrahim Muhammad
anajan daraktan ta kamfanin tuntuɓa na Jami’ar Khalifa Isyaka Rabi’u da ke Kano, Dokta Naja’atu Bala Rabi’u ta ce, an buɗe kamfanin ne domin saye da sayarwa da ƙirƙirar abin da babu, ko saye da sayarwar kaya ga Jami’ar kamar yadda suke a halin yanzu, amma nan gaba za su iya faɗaɗa shi zuwa wajen ta a matsayin kamfani.
Ta bayyana haka ne da take ƙarin haske ga ‘yan jarida ta ce sannan kuma suna yin ƙananan kwasa -kwasai da bita da bayar da horo ga ‘yan kasuwa da ɗalibai da ƙungiyoyin masu sana’o’i da sauran mutane ya danganta da buƙatarsu, ko da ba sa yin irin horon da ake nema za su iya haɗin kai da wanda ke son a yi horon su haɗu a dauki nauyin a gayyato masana a duk inda suke a gudanar a Jami’ar in an kammala za a ba da shaidar ka zo ka yi horo ko bita a Jami’ar.
Ta kara da cewa suna kuma da niyyar shirya kwasa- kwasai na takaitaccen lokaci na bayar da shaidar Diploma cikin wata shida ko wata uku nan gaba wanda shaidar diplomat zai ba da damar samun shiga Jami’a, amma yanzu suna jiran samun sahalewa ne kafin su soma. Abin da suke yanzu shi ne ba da shaidar satifiket, ba su soma na Diploma ba,”
Dakta Naja’atu ta ce hatta gwamnati suna so su sami dangantakar da za su riƙa ɗaukar nauyin ba da horo ga ma’aikata a fannoni daban-daban na gwamnatin jiha da na ƙananan hukumomi, kuma za su fifita ba da horon ne da harshen Hausa, amma a ba da shaida ta Jami’ar a kan duk horo da aka gudanar a Jami’ar ta ƙarƙashin ofishin na tuntuɓa.
Dakta Naja’atu Bala Rabi’u ta ce wannan tsarin tuntuɓa na Jami’ar da yake kamfani ne mai zaman kan shi a ƙarƙashin jami’a yake,ba shi da damar yin digiri, a karkashin su duk wani abu da zai samarwa da Jami’ar kuɗi sune da alhakin samarwa ban da wanda take samarwa daga ɗalibai, amma na yau da kullum zai zama a ƙarƙashin su, hanyoyi shigowar kuɗi a Jami’ar daga saye da sayarwa da yin duk wani abu da zai samar da kuɗaɗe duk akansu yake .
Ta bayyana cewa ba su bambanta da sauran jam’i’oi da yawa ba da suka daɗe, saboda sun sami wani jagoranci daga wasu jami’o’i sun je wajensu sun yi magana da su sun ba su shawarwari sai suka zo suna kwaikwayonsu da kuma ƙara tasu basirar a kai.
Dakta Naja’atu Bala Rabi’u ta yaba da irin ƙoƙarin mataimakin shugaban Jami’ar na KHAIRUN, Farfesa Abdulrashid Garba ta ce shi ne asali ya goya musu baya wajen ƙirƙirar sashen tuntuɓar da ƙaddamar da shi ya riƙa hoɓɓasa a kai wajen samar da cibiyar domin yin abubuwa na kasuwanci da za su samar da kuɗi don ragewa masu Jami’ar nauyi da yake kansu.
Ta ce duk kuɗi da ake samu yanzu daga ɗalibai ne, kuma abin da ake musu baya wuce a kashi 100 ya yi musu 10 ba. “Duk abin da suke na yau da gobe a hannun masu makaranta yake fitowa.”
Sai ya ce sun fito da sabon tsari da zai zama ana iya samar da wani kuɗin ban da wannan ta ina? Ya ga jami’o’i suna yi tunda shi daga Jami’ar Bayero yake, har ya yi mataimakin, mataimakin shugaban Jami’ar da kuma riƙon mataimakin shugaban Jami’ar ta Bayero saboda haka yake ganin su kwaikwayi jami’oi da suka daɗe, su ma su fito da wani tsari na shigowar kuɗi don tallafawa gudanar da makarantar.
Dakta Naja’atu Bala Rabi’u ta ce su yanzu suka fara, ba su soma samun komai ba daga tsare-tsaren su, suna fatan nan gaba burinsu zai cika za su sami abin da za su riƙa tallafawa su rage wa masu Jami’ar nauyi.








