Tsaffin Ɗaliban Kwalejin Ilimi Ta Tarayya Ta Kano ‘Yan Ajin 2004 Sun Yi Taro

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban da suka gama Kwalejin Ilimi ta Tarayya FCE da yanzu aka mayar da ita Jami’ar Ilimi ta Tarayya ta Kano ‘yan ajin shekarar 2004, sun gudanar da taron sada zumunci.

Sadiƙ Maitama Ahmad, wanda shi ne shugaban kwamitin shirya taron, ya bayyana cewa sun jima da kafa ƙungiyar, amma ba ta samu kafuwa sosai ba, sanadiyyar an rarrabu, kuma yawanci hankalin ɗaliban bai zo kan hakan ba a lokacin saboda ba a ɗauki shekaru da yawa ba.

Ya ce, amma sai yanzu da yake an ɗauki dogon lokaci mutane an soma girma an sami matsayi daban-daban a rayuwa, dalili ke nan da suka sake haɗuwa suke yin taron, wanda a baya ana samu ajujuwa daban-daban sukan yi nasu a rabe, amma yanzu sai suka ga cewa su haɗe gaba ɗaya na ‘yan shekarar ko daga wane aji ka zo, in dai a shekarar ta 2004 ka gama, ya kamata su haɗu tare domin su zama tsintsiya maɗauri ɗaya.

Ya ƙara da cewa Allah ya albarkaci ‘yan ajin nasu, domin suna daga cikin ɗalibai na FCE da suke da manyan sojoji da ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa da Malamai, har ma da Farfesoshi, kuma suna da mutane masu sana’o’i na hannu.

Ya ce, sannan sun yi ruwa da tsaki su ga cewa ya za su taimaka wa ‘yan uwansu, domin dama shi irin wannan taron ana yin sa ne, a kan abubuwa uku ya za a yi a taimaki ‘yan ajin ku, kai ka sani wane yana da ƙoƙari ya ma fi ka, amma dama ce Allah ya ba ka kai ka samu wani abu da ya fi nasa, to ya za a yi a taimake su a taimaki iyalansu.

Ya ƙara da cewa, bayan haka kuma akwai Malamansu waɗanda sun yi ritaya, wasu sun tsufa su ma ya za su yi su taimaka, musu hatta ita makarantar da suka amfana da ita wane irin tagomashi za su iya yi mata, waɗannan taimako duka suna yin su wasu a buɗe wasu ɓoye.

Sadiƙ Maitama Ahmad ya kuma bayyana cewa, yana daga abin farin ciki da suke cike da shi a yanzu da Kwalejin FCE ta koma Jami’a, saboda su a lokacinsu sun fara daga pre-NCE ne suna ciki suka yi NCE, to yanzu ta zama Jami’a, wanda yanzu ma kusan ‘yan ajin su guda 11 duk lakcarori.

Ita ma Ma’ajin ƙungiyar, Libabatu Sani Galadanci ta ce, taron sai godiya ga Allah, domin abin da ba su yi tunani ba, an zo an sami haɗin kai sosai, kuma mata ‘yan uwa sun ba da gudunmuwa wajen nasarar taron.

Shi ma ɗaya ɗaya daga mambobin ƙungiyar ɗaliban da suka gama FCE Kano a 2004, Malam Nasiru Aminu ya ce yana mutuƙar farin ciki sakamakon duba da yanayi na rayuwa da aka shiga, amma cikin hikimar Allah daga cikinsu ya kai wasu manyan matakai.

Ya ƙara da cewa a yau ya ga mutane da suka yi shekaru 20 ba su haɗu ba da bai san iyakar su ba, sannan kuma ya samu fahimta da ganewa, waɗanda tare suke, amma Allah ya sa suna cikin yanayin rayuwa, wannan na daga abubuwan da suka ja hankalinsu.

Daga nan Nasiru Aminu ya yi kira ga waɗanda suka gama Kwalejin a 2004 su juyo su waiwayi ƙungiyar tasu, ba don komai ba sai domin a taimaka wa ‘yan uwan da aka yi karatu da su aka yi zama na amana da mutunci.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe