Daga Khalid Idris Doya
A wani ibtila’in da ya faru a ranar Idi a jihar Gombe, wasu ƙananan yara biyu (mata) sun rasa rayukansu a babban filin Idin Gombe biyo bayan faruwar wani turmutsitsi.
Wakilinmu ya labarto cewa lamarin ya faru ne wajajen ƙarfe 10:45 na safiya jim-kaɗan bayan kammala sallar nafila mai raka’a biyu ta karamar Sallar 2025 wanda babban limamin Gombe ya jagoranta kuma gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar suka halarta.
Ɗan rahotonmu ya labarto cewa turmutsitsin ya faru ne a kofar fita yayin da jama’a suke ta ƙoƙarin fita daga filin Idin.
An kuma tattaro cewa wasu ƙarin masallata su 20 sun jikkata bayan biyu da suka rasu.
Rundunar ‘yansandan jihar Gombe ta bakin kakakinta Buhari Abdullahi, ta tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, akwai ɗimbin jama’a da suka haɗa da mata da ƙananan yara da suka yi ta ƙoƙarin gaggawar ficewa daga filin Idin, wanda tare da tsananin zafin da ake yi, hakan ya kai ga haifar da turmutsitsin.
“A sakamakon hakan, mutum 22 ne lamarin turmutsitsin ya shafa.
“Cikin gaggawa motar ɗaukar marasa lafiya daga gidan gwamnati ta kwashi waɗanda suka raunatan zuwa asibitin Zainab Bulkachuwa, yayin da sauran bakwai kuma aka kaisu zuwa asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya da ke Gombe domin nema musu kulawar likitoci.
“Abun takaici, mutum biyu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa likita ya tabbatar da mutuwarsu a lokacin da suke karɓar magani, su ne masu suna: Aisha Salisu Ahmed, ‘yar shekara hudu da rabi a duniya da kuma Maryam Abdullahi Gwani, ita ma ‘yar shekara 4,” ya shaida.
Rundunar ta bai wa masu kula da filin Idin shawara da cewa a nan gaba suke tabbatar da sun bude dukkanin ƙofofin wurin domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin a nan gaba.






