Na Ɗauki Darasin Rayuwa Mai Yawa A Wajen Marigayi Galadiman Kano -Ahmad Rabi’u

Daga Ibrahim Muhammad

Babban Daraktan Gudanarwa na Tashar Tsandauri ta Dala, Alhaji Ahmad Rabi’u ya bayyana marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi da cewa mutum ne mai haƙuri, tawakkali da dattako.

Ya ce sun yi ailki da marigayin kusan shekaru 40 da suka wuce, yana shugaban mayankar Kano, shi kuma yana wakiltar Alhaji Aminu Ɗantata a matsayin darakta a mayankar.

Alhaji Rabi’u, wanda kuma kuma tsohon shugaban cibiyar ciniki, kuma tsohon Kwamishinan kasuwanci na jihar Kano ne, ya ƙara da cewa ya koyi abubuwa masu yawa da suka haɗa da haƙuri da jagoranci daga gare shi.

Ya tabbatar da cewa ya ɗauki darasi mai na rayuwa da suka haɗa da na haƙuri da tawakkali a kan komai.

Alhaji Ahmad Rabi’u wanda tsohon babban Akanta ne na Alhaji Aminu Ɗantata ya ce, zaman da su ka yi na aiki da Galadiman Kano, Abbas Sanusi ya ga yadda yake jagorantar zaman su na daraktoci in al’amura suka taso yana fuskantarsu ya ba su dama a matsayinsu na matasa a lokacin su faɗi ra’ayinsu a kan abin da suke ganin ya dace, kuma ya karɓa.

Alhaji Ahmad Rabi’u ya ce a lokacin marigayi Galadima ya haɓɓaka mayankar Kano a matsayinsa na jami’in hukumar Native Authority, kuma mutum ne da ya ba da gagarumar gudunmawa wajen cigaban masarautar Kano.

Ya yi kira ga iyalan Galadiman Kano marigayi Abbas Sanusi a kan yin haƙuri da riƙe zumunci da yi masa addu’a a koyaushe.

  • Related Posts

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Asibitin Ƙashi na Tarayya da ke Dala, Kano, ya ba wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi, Hon. Abba Kabir Bichi, lambar karramawa bisa gudunmawa…

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gidauniyar NNPCL, reshen ayyukan jin ƙai na NNPC Ltd, ta ƙaddamar da sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani mai ƙarfin 1.5 Tesla MRI Scan da aka…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity