Cibiyar BGHP Da Haɗin Gwiwar Babban Sakataren Ma’aikatar Jinƙai Na Tarayya Adamu Ƙofar Mata Sun Raba Kekunan Guragu 100 A Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Babban Sakataren Ma’aikatar Jinkai na Tarayya, Alhaji Adamu Ƙofar Mata tare da haɗin gwiwar Beautiful Gate Handicapped People’s Centre Jos, sun raba kekunan guragu ga mutane 100 masu buƙata ta musamman ƙarƙashin ƙungiyar ci gaban Ƙofar Mata.

A yayin bikin rabon da aka gudanar a Unguwar Ƙofar Mata, Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Kano, Hon. Yusuf Ƙofar Mata ya yaba wa ƙoƙari da karamcin sakataren din-din-din na Ma’aikatar Jinƙai na Tarayya, Alhaji Adamu Ƙofar Mata, wanda ya zo da aikin da haɗin gwiwar Beautiful Gate Centre.

Ya ce an yi wannan ƙoƙari ne ta hanyar zaɓo masu buƙata ta musamman daga Ƙofar Mata da kewaye ta yi nasarar ba su kekuna masu ƙafa uku guda 100, wanda hakan ya nuna cewa mutane da dama za su a ci gajiyar shirin.

Ya ce a madadin al’ummar unguwannin Ƙofar Mata, Zango, Zage, Ɗorayi A da B sun yi matuƙar godiya da irin wannan shiri da Beautiful Get Handicapped People’s Centre da sakataren din-din-din na Ma’aikatar Jinƙai ta Ƙasa, Alhaji Adamu Ƙofar Mata, suna fatan sauran jama’a a cikin al’umma za su ci gaba da ba da gudunmawa wajen ci gaban al’umma da don abin da suke da shi domin kowane mutum yana da abin da zai ba da gudunmawarsa ga ci gaban al’ummarsa ko da nasiha mai kyau ne.

Saundra Yilgwan darektan yaɗa labarai na Beautiful Gate Handicapped People’s Centre, Jos yayin da take zantawa da manema labarai ta ce bikin rabon kekunan masu ƙafa uku na hadin gwiwa ne tsakanin Beautiful Gate Handicapped People’s Centre da sakataren din-din-din na Ma’aikatar Jinƙai da Kula da Bala’o’i, Dakta Yakub Ƙofar Mata don ba da kyautar kekunan guda 100 ga naƙasassu a Ƙofar Mata da kewaye.

Ta ce irin haɗin gwiwar da suka yi da sakataren na din-din-din, wanda shi ne ya nemo mutanen da ke buƙatar kayayyakin sannan ya ba su jerin sunayen domin su samar da kayan ga waɗanda suka ci gajiyar kuma sun ba su kekunan guda 100.

Sundra ta ce suna ba da kayan kyauta ne ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin, saboda sun lura cewa mai buƙata ta musamman wasu daga cikinsu da ƙyar suke zama kuma ba su da lokacin zuwa makaranta ko wani abu. “Don haka abin da za mu iya yi shi ne a ba da agaji abin da ake buƙata ta farko ita ce ƙarfafa mana gwiwa shi ya sa muke ba da wannan. An samar da dukkan kayayyakin a ofishinsu da ke Jos. Sannan kuma kuɗin da muka haɗa wa kowane ɗaya ya kai N160,000,” in ji ta.

Jami’a sashen watsa labarai ta Beautiful Gate Handicapped People’s Centre, Jos, Sandra Yilgwan ta ce ƙungiyar mai zaman kanta ce, kuma ta Kiristaci ce, amma ba sa nuna bambanci saboda kashi 80 cikin 100 na masu cin gajiyar Musulmi ne, har ma suna da ma’aikata Musulmi. “Ba su damu da irin addinin da kake ba ko imaninka, ko kuma sashen da kuka fito. Shekaru 20 ke nan da kafa cibiyar, yanzu haka mun raba kekunan guragu sama 40,000 kyauta da sauran kayayyaki ga masu buƙata ta musamman.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun