Babban Asibitin Anka Ya Sami Tagomashin Gwamna Lawal

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Gyararren Babban Asibitin Anka, Ya Tabbatar Wa Mutanen Zamfara Samun Nagartaccen Kiwon Lafiya

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa al’ummar Zamfara ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya kuma mai rahusa a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar yayin da yake ƙaddamar da Babban Asibitin Anka da aka gyara da kuma aka saka kayan aiki na zamani.

Gyaran Babban Asibitin Anka ya haɗa da tsohon sashen mahukunta asibitin, ɗakunan kwantar da marasa lafiya maza, ɗakunan kwantar da marasa lafiya mata, ɗakin bada magani, sabon get don tsaron asibitin, zauren da ya haɗe ɗakin mata, sashen X-ray da ɗakin tiyata, da sabon ginin sashen kula da haɗari da rashin lafiya na gaggawa, ɗakin gwaje-gwaje, sashen kula da ido da haƙori, da sashen mata masu juna biyu da tsohon ɗakin gwaje-gwaje.Sauran sassan da aka gyara da kuma saka kayan aiki sun haɗa da sashen Kulawa da Mata (ANC), ɗakin tiyata, ɗakin X-ray, sabon ginin hukunta asibiti, masallaci, gidan Babban Daraktan Lafiya (gidaje mai ɗakuna 3), da kuma sashen kula da yara, da dai sauransu.

A yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, an kammala gyaran gine-ginen tare da sanya dukkan kayan aikin kiwon lafiya cikin kwangilar cikin watanni 12.

Gwamnan ya ce, “A shekarar da ta gabata ne aka fara gyaran wannan asibitin, kuma wani kamfanin cikin gida ne aiwatar da kwangilar.“Saba hannun jarin ya mayar da asibitin zuwa wurin kiwon lafiya na zamani tare da na’urori na zamani, wannan ba shakka zai inganta jinya ga ‘yan jihar a garin Anka da kewaye.“Ga al’ummar Anka da kewaye, wannan aiki na ɗaya daga cikin alƙawuran da muka ɗauka na samar da ribar dimokuraɗiyya da inganta rayuwar ‘yan ƙasa.

“Za mu ci gaba da ba da fifiko kan al’amuran ci gaba, tare da tabbatar da cewa al’ummarmu sun samu ingantaccen lafiya kuma da araha, ilimi, noma, hanyoyi, da sauran muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar nan.

“Zuwa ga ma’aikata da mahukuntan babban asibitin Anka, ina kira gare ku da ku tabbatar da gudanar da wannan cibiya mai inganci da kulawa, ina kuma roƙon ku da ku jajirce wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’armu.”

Related Posts

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength