Ɗan Majalisa Zai Gina Ɗakin Jarabawa A Makarantar Sakandaren Gwamnati A Kano

Daga Ibrahim Muhammad

Ɗan Majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Tarauni, Hon. Kabiru Ɗahiru Sule ADS ya yi alƙawarin gina wa makarantar Sakandaren gwamnati ta Unguwar Gano Masallaci da zauren jarabawa a harabar makarantar kafin ƙarshen shekara.

Ya bayyana hakan ne da yake jawabi a yayin taron ranar bayar da kyautuka ga ɗalibai da aka gudanar a harabar makarantar ranar Laraba bayan ya karɓi lambar yabo da makarantar ta karrama shi da ita

Ɗan Majalisar dai ya ƙara da ɗaukar nauyin biya wa ɗalibai masu hazaƙa guda 600 da za a sanya aji na musamman na makarantar kuɗin rijista da za a zaɓo su daga gidajen masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya biya ba a yankin ƙaramar hukumar, inda ya ba da kuɗin ₦300,000 nan take, tare da alƙawarin bayar da bencina na zaman ɗalibai guda 20 zai kuma yi ƙoƙarin kawo cibiyar yin jarabawar JAMB a makarantar.

Ya ce ilimi shi ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma da suke koyi da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ba shi goyon baya a tsarin da ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a kan ilimi duba da ilimi na kowa ne za su yi ƙoƙarin taimakawa daidai da ikonsa.

Hon. Kabiru Ɗahiru Sule ya bayyana irin ɗimbin ayyuka da ya gudanar a mazaɓun ƙaramar hukumar daban-daban kama gina daga gina rukunin ajujuwa da kuma gyaran makarantu da gina masallatai da cibiyoyin addinin Musulunci.

Shi ma a jawabinsa tunda farko shugaban makarantar Sakandaren gwamnati na Unguwar Gano, Malam Auwalu Ali Yalwa ya bayyana taron da cewa shi ne na farko na raba kyautuka ga ɗalibai masu ƙwazo da aka yi a makarantar da ya sami halartar ɗan Majalisar jiha na Tarauni da kansilan mazaɓar Unguwar Gano wanda shi ne ya wakilci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Hon. Ahmad Sekure.Itama shugaban ƙungiyar shugabannin makarantun Sakandire na jihar Kano, Hajiya Uwani Ahmad Balarabe da mutane da dama sun halarta.

Ya ƙara da cewa zuwan sa’a matsayin shugaban makarantar ya sami kyakkyawan haɗin kai daga malamai suna aiki tare don cigaban makarantar kuma shi ne ya bijiro da tsarin fara yin Sallar Azahar a jam’i ga ɗalibai a makarantar.

Sannan ta zama cibiya ta yin jarabawar WAEC da NECO da wasu makarantun ma za su zo su yi a nan.

Shugaban makarantar Sakandaren gwamnatin na Unguwar Gano ya ce yanzu suna da ƙarancin ajujuwa da rashin zauren jarabawa da kuma abin zama da masallaci wanda sun ji daɗin ɗan majalisar jaha, Jon Kabiru Ɗahiru Sule ADS da ya halarci taron ya yi alƙawarin gina musu sannan tsohon shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Habib Zakari shi ma ya yi alƙawarin kawo musu allo na zamani wanda wannan babban nasara ce a gare su suna kuma kira da a zo a samar musu rijiyar burtsatse saboda sai sun fita wajen makarantar suke samun ruwa.

Malam Auwal Ali Yalwa ya yaba da haɗin kai da iyaye suke ba su ta yin iya ƙoƙarinsu, musamman ta yadda suke tiritiri da ‘ya’yansu wajen zuwa makarantar, yana fata za su cigaba da juriya da ba da kulawa sosai, ya kuma nemi al’umma su cigaba da ba su haɗin kai.

A yayin taron makarantar sakandaren gwamnatin ta Unguwar Gano ta karrama mutane da dama da lambar yabo bisa gudummawa da suke bai wa bunƙasa cigaban ilimi ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Tarauni, Hon. Ahmad Sekure da Hon. Kabiru Ɗahiru Sule ɗan Majalisar jaha da shugabar ƙungiyar ANCOPSS ta jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da Malaman makarantar masu hazaƙa.

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe