Zamu yi aiki da Kasar Sweden don amfanin Al’ummar Zamfara – Dauda Lawal

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa a shirye ya ke ya haɗa hannu da ƙasar Sweden a fannoni da dama, waɗanda suka haɗa da ilimi, Harkar lafiya da samar da makamashi.

Gwamna Lawal ya furta haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ambasadar ƙasar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund cikin makon da ya gabata a ofishin sa da ke Abuja, inda ziyarar ta bayar da dama wajen tattauna muhimman batutuwa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Gwamnan ya riga ya fitar da matakan jawo masu zuba jari da tallafi daga ƙasashen waje.

Sanarwar ta Idris ta ce, “A makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin Ambasar ƙasar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund a ofishin sa da ke Abuja.

“A tattaunawar ta su, sun tattauna batutuwa da niyyar samar da haɗin gwiwa a muhimman fannoni na tattalin arziki, ƙulla kyakkyawar dangantaka da samar da manyan ayyuka don amfanin jihar Zamfara da Zamfarawa.

“Gwamna Lawal ya kuma ƙara tabbatar wa da baƙuwar tasa cewa a shirye gwamnatin sa ta ke wajen haɗa hannu da Sweden don samar da ci gaba a fannoni da dama.

“Ƙasar Sweden ta nuna buƙatun ta na haɗa hannu da jihar Zamfara na samar da dangantaka mai ɗorewa, tare da aiwatar da ayyukan ci gaba don amfanin al’ummar jihar a Nijeriya.”

Bugu ta ƙari, Ambasadar ta yi alƙawarin samar wa Zamfara masana a harkar haƙan ma’adinan ƙasa, dabarun noma na zamani, tallafawa don inganta ilimi, harkokin kiwon lafiya da samar da hasken wutar lantarki na Sola.

Related Posts

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History