Daga Ibrahim Muhammad
Gwamna jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar da yake jagoranta murnar shigowa sabuwar shekara da yi masu fatan samun ci gaba a 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai.
Gwamnan ya yaba da juriya da haƙurin da mazauna Kano suka nuna wajen tunkarar ƙalubalen da suka fuskanta a 2024, tare da tabbatar musu da jajircewarsa na ganin ya samar da ci gaba mai ɗorewa a 2025.
Ya yi wa al’ummar jihar Kano barka da shigowa sabuwar shekar, tare da fatan 2025 ta zama shekarar aminci, zaman lafiya, wadata, da ƙarin hadin kai.
Sannan ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin inganta rayuwar ‘yan jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wajen ganin an amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 a kan lokaci. “Wannan wani muhimmin mataki na haɓɓaka cigaba a faɗin jihar.
Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa jihar Kano za ta samu cigaba a fanni samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da noma a sabuwar shekarar nan.
Ya kuma bayyana shirye-shiryensa na kammala ayyukan tituna da ake ci gaba da yi a jihar, da faɗaɗa cibiyoyin kiwon lafiya, da inganta harkar ilimi, da tallafa wa manoma da kayan aiki don bunƙasa noman abinci da rage tsadar kayan abinci.
Tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na bunƙasa rayuwar matasa da mata ta hanyar koya musu sana’o’i da kuma ƙara samar da rance ga ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa don ciyar da tattalin arziƙin jihar gaba.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnatinsa haɗin kai da goyon baya a ƙudirinsa na kai jihar tudun mun tsira.
Ya yi fatan shekarar nan ta 2025 za ta zama wacce za a sami sauyi da samar da ingantacciyar rayuwa da damammakin tattalin arziƙi a kowane lungu da saƙo na jihar Kano.






