Abin Da Ya Sa Muka Shirya Wa Limaman Masallatan Juma’a Na Jihar Kano Taron Bita -Ibrahim Waiya

Daga Ibrahim Muhammad

Ma’aikatar yaɗa labarai da al’amuran cikin gida, ta gudanar da taron bita na kwanaki biyu ga limaman Juma’a na jihar Kano domin tunatar da su wajibin da ya hau kansu.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan kammala taron bitar na kwanaki biyu, Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa a matsayin Ma’aikatar da take da haƙƙi wajen yaɗa labarai da sanar da al’umma abin da ya shafi ayyuka da tsare-tsaren abubuwa da gwamnatin jihar Kano take gabatarwa da ƙoƙarin samar da dangantaka tsakanin kowane rukuni na al’umma a madadin gwamnatin Abba Kabir Yusuf suka ga dacewar yi wa limamai irin wannan bita.

Ya ce bitar za ta ƙara samar da fahimtar juna ta nusar da su kan abin da ya shafi ayyuka na gwamnati domin samun ilimi na yadda al’amuran gwamnati ke gudana yadda za su iya sanar da mutane yadda abubuwa ke gudana.

Ya ƙara da bayyana bitar da cewa wata gada ce aka shimfiɗa da za ta zama an yi ƙoƙarin tsuke tsayin dangantaka da ke tsakanin gwamnati da dukkan rukunin al’umma kuma za su cigaba da kulla tattaunawa da limaman daga lokaci zuwa lokaci tsakaninsu, wannan kawai farawa aka yi.

Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce sun ɗaukarwa kansu gabatar da tattaunawa da dukkanin rukuni na al’umma don tabbatar da cewa an ɗinke duk wata ɓaraka ta rashin samun fahimta a kan abin da yake gudana a gwamnati ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Kwamishinan Ma’aikatar, ya bayyana malamai a matsayin mutane mahimmai masu daraja da ya zama wajibi ga al’umma su mutunta su girmama su domin suna sanye da riga muhimmiya da ba a iya sayen ta a kasuwa riga ce da take siffanta su a matsayin magada Annabawa mutane ne da ake sa ran duk abin da zai fito daga bakinsu da ayyukansu, ya zama abin da zai nusar da al’umma shiriya kar ya zama abin da zai rikita lissafi ko ya zama abin da zai iya tayar da fitina ko wani abu makamancin haka a tsakanin al’umma.

Ya ce ya kamata malamai su fahimci muhimmancin da suke da shi a cikin al’umma. b Ba sa son duk abin da zai taɓa kimar su. Suna kishinsu, sun damu da su suna son su tabbatar duk abin da za su aikata da abin da za su faɗa ya yi daidai da koyarwa ta addini ba son rai ba.

Ya ce gwamnatin jihar Kano za ta cigaba da girmama malamai da ƙulla kyakkyawar alaƙa da su, don su zama tsani wajen faɗakar da al’umma irin abubuwa da ake a gwamnatance domin mutane su fahimci yadda aikin gwamnati yake da yadda ake gudanar da wasu abubuwa.

Kwamishinan ya ce shi ya sa suka kawo mutane daban-daban suka wayar musu da kai a taron bitar kan abin da ya shafi harkoki na mulki a tsari na dimokwaraɗiyya su gane ya ake kasafin kuɗi, kuma waɗanne abubuwa gwamnati take shigowa da su sababbi wajen kyautatawa da samar da kyakkyawan shugabanci a cikin al’umma, musamman a kan abin da ya shafi ƙoƙarin da take yi na kawo ƙarshen almundahana da dukiyar mutane.

Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya ya ja hankalin Limaman da aka yi wa bitar da cewa bai dace wasu daga cikinsu su riƙa amfani da mumbarinsu wajen yin abubuwa na siyasa ba. “Kowane Malami ya kamata ya bar ra’ayinsa na siyasa a zuciyarsa, idan ya hau mumbari ya fahimci cewa yana wakiltar dukkanin rukuni ne na al’umma ne ba tare da nuna ra’ayi na siyasa ba,” ya jaddada.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe