Abin Da Ya Sa Na Fito Neman Shugabancin Ƙungiyar Kasuwar Waya Na Titin Beirut -Dan’aljannah

Daga Ibrahim Muhammad

Hon. Isah Garba Dan’aljannah tsohon sakataren na kasuwar waya na titin Bairut, kuma mataimakin ƙungiyar masu waya da dangoginta ta Nijeriya AMPAT da sama da shekaru 20 yana kasuwar ya kuma riƙe muƙamai da dama a cikin ta kama daga jami’in hulɗa da jama’a da mataimakin sakatare da sakataren Hukumar zaɓe wanda ya ba da gudunmuwa a cikin kasuwar wajen kawo cigaba da zaman lafiya.

Ya amsa kiran da ‘yan kasuwar waya na titin Bairut suka yi.

Masa na fitowa neman takar shugabancin ƙungiyar da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan kira da aka yi masa Hon. Isah Garba ya ce ba sabon abu ba ne, idan an yi kiran sa ya zo ya nemi shugabancin ƙungiyar kasuwar, idan aka yi la’akari da irin mutane ya gina da taimakawa, ƙanana suka miƙe waɗanda ba su da sana’a suka sani wajen sana’a da kasuwanci don haka idan suka shuka alheri shi ake girba idan akasin haka suka shuka shi za ka gani don haka wannan kira da aka yi masa ya fito yana neman wannan shugabanci na kasuwar.

Ya yi nuni da cewa a yanzu kasuwar tana fuskantar ƙalubale da suka soma zuwa musu, da babu su a baya shekaru 18 da suka gaba ta.

Cikin manyan ƙalubalen akwai samun matasa da suke shigowa kasuwar suke nema su gurbata musu tsohon tarihi da suke da shi na zaman lafiya da mutuntaka, sanin sakamata da kasuwanci cikin aminci, amma a wadannan shekaru uku sun soma ganin canji sakamakon matasa da suke zuwa kasuwar daga wasu wurare ba tare da an yi musu rijista ba, suna kasuwanci wanda suka soma haddasa musu rashin amana a cikin kasuwar da ake yawan samun matsaloli hakan na barazana ga cigaban kasuwar.

Ɗan’aljannah ya ce dole aƙalla wannan abin ya zama an mayar da kasuwar kan tsari da take na asali duk wanda ya zo sai sun san daga ina yake, me ya kawo shi kasuwa, me zai yi su waye abokan mu’amalarsa, domin su cigaba da riƙe kambun suna kasuwa mafi tsafta a ƙasar nan a kan abin da ya shafi hada-hada na harkar waya cikin aminci da gaskiya.

Game da rashin samun babban dila na kamfanin waya a Kano ya yi nuni da cewa duk da mutane suna ƙorafi da hakan, amma nuna sha’awar ka ga abu shi zai sa kamfani ya yi maka dila ba kamfanin da zai ɗauki dila ya ba ka ka yi sai ka nema, kuma yin dila yana da kuɗi da yawa, mutanen su suna gani ba za su iya cire waɗannan kuɗi su je su ajiye a kamfani domin a ba su dila ba.

Ya ce domin ƙarƙashin neman dila idan kana so ka zama sai ka ajiye Dala Miliyan1.5. kuɗi ne da ya haura Naira biliyan ɗaya da rabi wannan za ka ajiye ne a matsayin “standing order.”

Na kamfani wanda shi zai ba ka damar a fara tantance ka a matsayin dila.

“Abu na biyu shi ne tsari na oda duk wata za ka yi oda sau uku wacce ta kai ta biliyan uku kuɗi ne da ake buƙatar sama da biliyan biyar kafin a ce ka sami dila na waya, mutanenmu wajen cika wannan ƙa’idojin yakan zaman musu mai wahala,” in ji shi.

Ya ce su sauran abokan zaman mu na Kudu sukan yi amfani da bankuna kasuwanci su karɓi kuɗaɗe a hannunsu su je su saka su a wannan yanayin a cigaba da kasuwanci, wanda mu kuma duba da al’ada da addini takan yi tasiri wajen mutane suna ganin bai kamata su karɓi kuɗin ruwa ba su je su saka shi a cikin irin waɗannan abubuwa, ya na daga cikin abin da ke jawowa ake ganin ‘yan Kano babu dila, amma magana ne na ƙa’ida ko a yanzu in akwai wanda ya cika wannan ƙa’idar yake so kuma a ba shi dila, suna da kyakkyawan alaƙa da kamfanonin gaba ɗaya a matsayinsa na mataimakin sakatare na ƙasa na ‘yan waya.

Sun yi zama ba ɗaya ba biyu ba, amma ba a sami wanda ya cika wannan ƙa’ida ba, matsalar ba na Kano ba ne ko yanzu aka samu wanda ya cika ƙa’ida kasa da wata biyu zai zama dila.

Isah Garba ya ce ɗaya daga ƙalubalen shi ne gwamnatocin Arewacin Nijeriya na da sakaci a kan waɗannan abubuwa, gwamnati ba ta taimakon ‘yan kasuwa yadda ya kamata abin da ya shafi kasuwanci su Kudu akwai ɗauki da suke samu daga gwamnatocin suna jihohi da ƙungiyoyi, amma sama da shekaru 20 da ya yi a kasuwar titin Bairut a gwamnatoci da akayi daban-daban ba wanda ya warewa ‘yan waya ya ba su tallafin ko da na N100,00.

Abu ne da ya kamata a zo da tsari ko da kananan bankuna ne da za su bai wa ‘yan kasuwa jari mara ruwa hakan zai taimaka ƙananan ‘yan kasuwa su yi ƙarfi ko a samu wani yanayi da gwamnati za ta yi haɗin gwiwa da ‘yan kasuwa ta tallafa musu su je su sami dila wannan har zuwa yanzu babu.

Hon. Isah Garba Ɗan’aljannah ya ce amma ba su sani ba wannan gwamnati ta jihar Kano ta Injiniya Abba Kabir Yusuf idan an yi zaɓe na ƙungiya ta su ta kasuwar titin Bairut ya yi nasara za su rubuta koke a kan wannan, domin su ga ko akwai abin da za a samu gwamnati ta shigo ciki ta ga yadda za ta taimaka a sami dila na waya a arewacin ƙasar nan.

Hon. Isah Garba ya ce shi wannan takara da ya amsa ya fito duk wani abu da zai yi na yaƙin neman zaɓe a shekaru 20 da ya shafe a kasuwar yana ba da gudunmuwa ba ya buƙatar ya ce ga abin da zai yi a gaba duk abin da za su yi idan na alheri ne al’umma sun gani in akasin haka nema sun sani, sai dai kiran sa ga al’umma shi ne ka da su kuskura su damƙa amanar dukiyarsu da kasuwanci su a hannun mutanen da ba su ma san mene ne kasuwancin ba, kuma ba su san ma ya ake mu’amala a shugabanci ba wanda yake kamar makaranta ce sai ka koya daga matakin koyo matakin iyawa zuwa na ƙwarewa ba zai yiwu ka faɗo daga sama ba ka san ina aka taso ba ina za a ba, ka zo ka ce ka fito takarar shugabancin al’umma a al’ummar da ba ka taɓa zama a cikinta ka fahimci ‘ya’ya al’amuranta yake ba sannan a yi tsammanin za a sami wani abu na ci gaba shawararsa duk wanda za a zaɓa a tabbatar da sun zaɓi wanda yake da kyakkyawar shaida na mutuntaka da ya iya mu’amala da kowa da kwatanta gaskiya da adalci don a sami cigaba.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe