Daga Ibrahim Muhammad
Ɗalibai sama da 2,000 ne suka sami shaidar Diploma bayan kammala karatu a fannin addinin Musulunci da suka gudanar a Africa Academy da ke ƙarƙashin Africa TV3.
Taron yaye ɗaliban an gudanar da shi ne a babban ɗakin yaye ɗalibai na sabuwar Jami’ar Bayero ta Kano ranar Asabar.
Dakta Habeeb Tijjani Tahir shi ne Manajan Daraktan na gamayyar tashoshin Africa TV da ta ƙunshi Afrika TV3 da Afrika TV3 Qur’an da Salam Afrika Radiyo da AD plus da Africa Academy, wanda a ƙarƙashinta ne aka yi karatun da bayar da shaidar Diploma a karo na farko.
Ya shaida wa ‘yan jarida cewa ɗalibai sama da 2,000 da suka yi karatu tsawon na shekara ɗaya a tsarin zango na ɗaya da na biyu ne da suka kammala aka yaye, kuma sun kuma fito da yin karatun ne duba da abubuwa da suka yi wa mutane yawa na harkokin rayuwa, shi ya sa aka fito da karatun da ake yi ta hanyar badarwar zamani 100 bisa 100.
Ya ce a matsayinsu na masu gudanar da harkar yaɗa labarai abin da ya ja hankalinsu ya sa suka bijiro da wannan koyarwa shi ne yadda suka ga jama’a na bibiyar su sosai suka ga suna kwaɗayin son ilimi na yadda za su bauta wa Allah.
Mutane suna son neman ilimin, amma saboda yanayi na ɗawainiya rayuwa da rashin lokaci ba ya ba su dama su yi karatu, shi ya sa aka fito da wannan tsarin ya taimaka musu wajen amfana wajen samun ilimi.
Dakta Habeeb Tijjani Tahir ya ce abin da ya sa ake yin karatun da harshen Hausa an yi duba ne da ƙasashen da suka cigaba a wannan zamanin suna amfani ne yarukansu na uwa suna koyar da ilimi hatta Kimiyya da Fasaha da yarukansu suke wannan ya sa sun sami cigaba, don haka suka ga mene ne amfanin ka je kana bai wa mutane wahala ta yin wasu yaruku da ba su ƙware a kai ba, kuma karatun addinin nan abu ne da ake so a fahimci shi a bauta wa Allah da shi.
Ya ba da misalin cewa akwai mace a gida da ƙila ba ta yi karatu ba, akwai dattijai da ba su yi karatu ba, wannan harshen nasu na Hausa da shi za a yi amfani domin a koyawa mutane ilimin addini su fahimci shi yadda ya kamata ba tare da sun sha wahala ba.
Ya ce da farko kafin su soma ba da shaidar Diploma daga shekara ta 2022 sun fara da kwasa-kwasai ne masu gajeren zango suna ba su shaidar satifiket, ɗalibai za su yi karatu a wani fanni na ‘yan makwanni ne a ba su shaida misali kamar a darasin Fiƙihun Sallah ko alwala koma a kan aikin Hajji shi za a koya wa ɗalibi ya yi jarabawa a ba shi takardar shaida a kai daga baya aka kawo ba shaidar Diploma.
Dakta Habeeb Tijjani Tahir ya ja hankalin ɗaliban da suka sami shaidar kammala karatun su yi aiki da abin da suka koya a wajen bauta wa Allah yadda ya dace, su kuma sabbin ɗaliban da za a ɗauka ya yi musu fatan alheri karatun ya yi musu amfani.
Bayan lada da za su samu har ma da al’ada ta kyautuka suka samu da aka bai wa ɗaliban da suka nuna hazaƙa, wanda ya zo na ɗaya an ba shi kujerar Umara, na biyu Dala 500, har zuwa kan na 10 an bai wa waɗannan kyaututtukan.
Malam Abdulƙadir Isma’il, ɗaya daga malaman da suka koyar da ɗaliban ya ce, karatu ta kafar sadarwa sabon tsari ne da ya zo a duniya tun lokacin annobar Korona da aka rufe duniya gaba ɗaya, sai karatu ya koma ko daga nesa mutum zai iya yi ta kafar sadarwa, tun daga digiri na farko da na biyu har digirin digirgir ana yin su a gama, kuma idan aka yi la’akari da yadda tattalin arziƙi yake mafi yawa ba za a iya zuwa su yi karatun, amma ta wannan tsarin sai su yi.
Ya ƙara da cewa tsarin zai ba da damar kana sana’arka, kana yin karatu ta wayarka ko a kwamfuta. Sannan a ware rana da za ka yi jarabawa. Wannan salo an fito da shi ne domin a taimaka ya zamana ba za a daina karatu ba, domin idan aka daina karatu al’umma ta lalace ke nan.
Malam Abdulƙadir Isma’il ya yi nuni da cewa sai dai wannan karatu ta kafar sadarwa har yanzu a tsakanin mutanenmu na Arewa abin bai karɓu ba sosai ba, saboda har yanzu wasu na shakka da kokwanto cewa anya kuwa karatun zai zamo mai inganci, ko kuma shaidar da za a ba shi za ta zama daidai da wanda ya je ya yi a gaban Malami a aji keke da keke har yanzu irin wannan tunanin mutane na buƙatar a wayar musu da kai cewa su yi wannan karatun shi ne salo na zamani, kuma yana da inganci kamar na yadda aka saba.
Shi ma a jawabinsa mataimakin babban kwamandan Hisba na jihar Kano, Sheikh Mujahideen Aminudeen ya yaba wa African Academy da dukkan masu ruwa da tsaki da yi musu fatan alkhairi ƙarƙashin Dakta Habeeb Tijjani Tahir bisa wannan karatu da suka gudanar kyauta, sannan ya ja hankalin manyan masu sukuni, jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa su shigo su taimaka su kuma ɗalibai da aka yaye, ya nemi su yi amfani da karatu da su ka yi da jin tsoron Allah kar a watsar da abin da aka koya.
Shi ma shugaban ɗalibai na African Academy Ishak Garba ɗaya daga waɗanda aka yaye ya gode wa Allah da gidan talabijin na Afirka 3 da Manajan Daraktan ta Dakta Habeeb Tijjani Tahir da sauran malamai da suka koyar dasu. Sannan ya yi kira ga sauran mutane su yi rijista a makarantar don akwai nasarori da za su fa’idantu da su kamar yadda suka amfana musamman a kan sanin addinin Musulunci.
Ɗaya daga cikin iyaye da ‘ya’yansu suka yi karatun aka yaye da shaidar Diploma, Ambasada Dakta Bashir Yusuf Pantiya ya yaba wa ƙoƙarin African Academy kan assasa wannnan karatun Diploma na ilimin addinin Musulunci a cikin harshen uwa ta fasahar sadarwa da zai zama alkhairi ga al’umma.
Ya ce tsarin karatun zai bai wa ɗimbin al’umma manya da matasa maza da mata dama ta sanin addini a kowane yanayi da ba sai ya tsayar da harkokin na yau da kullum ba, kama daga masu aikin gwamnati ko na kamfani ko masu safara.
Ambasada Dakta Bashir Yusuf Pantiya, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar kasuwar Singa da aka fi sani da SIMDA a matsayinsu na ‘yan kasuwa ya yi kira ya ‘yan kasuwa su rungumi wannan hanya ta yin karatu ta hanyar kafar sadarwa daga inda suke a daga zai ba su dama sosai wajen samun ilimi.
Taron ya sami halartar Hakimin gundumar Gobirawa, Alhaji Harazumi da malamai da ‘yan kasuwa.
An karrama Manajan Daraktan African TV3, Alhaji Habeeb Tijjani Tahir da malamai da ɗalibai da sauran mutane da lambar yabo bisa yabawa da ƙwazonsu.








