Daga Ibrahim Muhammad
A wani labari da muka samu an bayyana cewa Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Ɗantata sun shaida cewa marigayin ya bar musu wasiyyar cewa duk lokacin da ya rasu a binne gawarsa a birnin Madina.
Ɗaya daga cikin iyalansa, kuma ‘yar’uwa ga uwargidan marigayin da ta rasu shekaru biyu da suka gabata, Hajiya Amina Umar Fulani ce ta shaida hakan a zantawarta ga ‘yan jarida a safiyar yau Asabar.
Ta ce marigayin ya ba da wannan wasiyyar ne tun bayan rasuwar matarsa Hajiya Rabi Tajo Ɗantata a Madina.
Alhaji Aminu da ya rasu a Dubai daga nan za a ɗauki gawarsa zuwa birnin Madina domin binne shi.







