Daga Ibrahim Muhammad
Sakamakon kyakkyawar shaida ta irin ɗimbin gudunmuwa da take bayarwa, Gidauniyar Hausa da haɗin gwiwar Hausawan Duniya Charity, ta tabbatar da Ambasada Hajiya Samira Bala Usman a matsayin Tauraruwar Hausa da cigaban Hausawan Duniya a wani taro da aka gudanar na Gidauniyar a Kano.
Da take zantawa da ‘yan jarida bayan karɓar shaidar, Hajiya Samira Bala Usman, ta bayyana farin cikinta da murna bisa shaida da aka ba ta ta zama ɗaya daga cikin ‘yan Gidauniyar Hausa da Hausawan Duniya Charity duba da yadda ƙungiya ce da take da himmar samar wa Hausawan Duniya haɗin kai da cigaba.
Ta ƙara da cewa ta gamsu mutuƙa da irin tsare-tsaren da Gidauniyar take yi masu ma’ana wajen gina cigaban al’umma.
Ta ce tana ƙoƙari wajen hana barace-barace da tallafa wa marayu da kuma haɗa kan al’ummar Hausawa a duk inda suka samu kansu a duniya, kowa ya san ɗan’uwansa sanan suna kuma bunƙasa al’adu da harshen Hausa.
Ambasada Hajiya Samira Bala Usman Tauraruwar ta Hausa da Hausawan Duniya ta yi nuni da cewa dama Gidauniyar ta Hausa da haɗin kan Hausawa na duniya tana da jajicewa wajen cigaban al’ummar Hausawa, kuma su ma da suke a cikinta za su ba da gudunmawa sosai domin kan Hausawa ya haɗu a ko’ina suke a kowace ƙasa a fadin duniya.






