Daga Ibrahim Muhammad
An ƙaddamar da littafin TAYA NI MU GYARA da ke ba da shawarwari ga ma’aurata da Malama Zuwaira Dauda Kolo ta wallafa.
Taron ƙaddamar da littafin an gudanar da shi ne a ɗakin taro na Gidan Mumbayya a ranar Asabar ya sami halartar mutane da dama daga ciki da wajen jihar Kano.
Ɗan Salanken Gaya, Alhaji Abdurrahman Muhammad, ɗaya daga cikin manyan baƙi da ya ƙaddamar da littafin ya bayyana cewa abu ne mai muhimmanci tallafawa irin waɗannan mata masu hazaƙa da suka wannan aiki na rubuta littafin don faɗakarwa, kuma za su riƙa ƙarfafa musu gwiwa a kai.
Da take zantawa da ‘yan jarida bayan ƙaddamar da littafin, marubuciyar littafin, Zuwaira Dauda Kollo ta ce, abin da ya ja hankalinta har ta kai ga rubuta littafin shi ne yawan matsalolin da ake samu na mutuwar aure, musamman a Arewa, da an yi ba ya jimawa sai a yi saki, shi ne ta yi rubutun don fito da abubuwa da suke wa aure kisan mummuƙe da gurgunta domin ba da gudunmawa a samu gyara.
Ta ƙara da cewa tana fata littafin da ta rubuta ya sami karɓuwa ta hanyoyi da dama, yadda mata idan sun karɓa a kafofin sadarwa na zamani da gidajen radiyo da jaridu a karanta littafin ya zama sila wajen bayar da gudunmawa wajen gyara zamantakewar aure.
Malama Zuwaira Dauda Kollo ta ce mataki na gaba bayan ƙaddamar da littafin shi ne a samu ya shiga makarantu musamman na kwana na ‘yan mata da na matan aure, gidajen matan aure da ƙungiyoyin mata waɗanda kuma ba za su iya karatu ba akwai hanyoyi na tuntuɓa da za su riƙa yi domin a riƙa sanar da su abin da littafin ya ƙunsa. Sannan ta nemi gwamnati ta tallafa domin littafin ya kai ga yara masu tasowa ‘yan mata a makarantu da za a riƙa karanta musu.
Marubuciyar littafin na TA YA NI MU GYARA shawarwari ga ma’aurata Zuwaira Dauda Kollo ta godewa ɗimbin manyan baƙi da sauran muhimman mutane da suka ajiye uzurorinsu suka zo domin halartar taron ƙaddamar da littafin, kuma ta gode wa dukkan waɗanda suka sa hannu wajen ganin littafin ya tabbata tare da ƙaddamar da shi.
Taron dai ya sami halartar fitattun marubuta a da suka haɗa da Ado Ahmad Gidan Dabino da Ibrahim Muhammad Indabawa da saura da dama.






