An Ƙaddamar Da Rabon Kayan Makaranta Kyauta Ga Ɗaliban Firamare A Fagge

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙaramar hukumar Fagge ƙarƙashin shugabancin Hon. Salisu Usman Masu za ta samar da masu gadi domin kyautata tsaron makarantun yankin.

Shugaban kansuloli na ƙaramar hukumar Hon. Sani Muhammad Scorer ne ya bayyana hakan yayin da ya wakilci shugaban ƙaramar hukumar a wajen taron ƙaddamar da raba wa yara ‘yan makarantar Firamare kayan karantu kyauta da gwamnatin jihar Kano ta samar.

Ya yi nuni da cewa aƙalla za a ɗauki masu gadi 50 da za su riƙa kula da makarantun domin hana ɓata-gari da suke shiga wasu makarantun suna ɗebe kayayyakin koyo da koyarwa da suke a cikinsu, sannan kuma za su kyautata yanayin jin daɗin ɗalibai da kuma malamai ta yadda za a riƙa koyo da koyarwa cikin walwala.

Hon. Sani Muhammad Scorer ya ce ƙaddamar da raba kayan makarantar ga ɗalibai ‘yan yara na daga cikin cika alƙawarin da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi lokacin yaƙin zaɓe na bai wa yara kayan makaranta da kuma ciyar da su da shi ma za a soma nan gaba kaɗan.

Ya ce kayan makarantar za a bai wa ɗaliban makarantun Firamare ne ‘yan aji ɗaya da aji biyu da na uku a halin yanzu domin ko a baya ma Gwamnan jihar Kano ya ƙaddamar da ba da kujeru ga ‘yan makaranta da aka raba a makarantun da suke yankin ƙaramar hukumar.

Ya ce Fagge tana tsare- tsaren da ya kamata domin kyautata harkar cigaban ilimi a fannoni da daban-daban domin shi ma shugaban ƙaramar hukumar ya yi koyi da Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen bai wa ci
gaban ilimi fifiko a yankin. Don haka nema muke kiran sa da ‘Mr. Education’.

“Sannan kuma ƙofarmu a buɗe take ga kowa da kowa musamman Ma’aikatar Ilimi ta yankin domin ba mu shawarar da za ta kawo cigaban ilimi,” in ji shi.

Shi ma a nasa jawabin, sakataren ilimi na ƙaramar hukumar ta Fagge,
Ibrahim Sallau ya bayyana mutuƙar farin cikinsa bisa ƙaddamar da rabon kayan makarantar guda 17,000 na maza da mata da aka samar, domin hakan zai taimaka sosai wajen bunƙasa cigaban ilimi a yankin. “Wannan irin manufa ce ta Jagora Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ta rabawa yara kayan makaranta da su ma suka bi umurnin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce a rabawa yara daga ‘yan aji ɗaya da biyu da uku kaya kyauta,” ya jaddada.

Ya ce yara da aka bai wa ‘uniform’ ɗin wasu ba kayan makaranta suke zuwa yau sai ga shi yara kowa da sabon kayansa zai koma gida. “Wannan na daga abin da zai taimaka wajen haɓɓaka ilimi a jihar Kano, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu game da manufofin Gwamna a kan ilimi,” ya tabbatar.

Sakataren ilimi Malam Ibrahim Sallau ya ce, Gwamna Abba Kabir na ba da kulawa ga malaman makarantu, musamman na Firamare wajen biya musu haƙƙoƙinsu da yi musu ƙarin girma da ƙari na shekara-shekara wanda a baya ba sa samun wannan. Yau malamai suna samun cigaba hatta shugabannin makarantu ana sa musu abubuwan da za su ƙara musu ƙwarin gwiwa a aikin su.

  • Related Posts

    WOTCOSA Ajin 1975 A Shekara 50: Sun Karrama Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje Da Tagwayen Lambobin Yabo

    Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban tsohuwar makarantar horon malamai ta mata ta Kano (WTC), Women Teachers College Old Girls Association (WOTCOSA) da yanzu ake kiran a makarantar da Goverment Girls College (WTC)…

    Ɗaliban Ƙaramar Hukumar Dala Da Gwamnatin Kano Za Ta Tura Manyan Jami’o’i Na Cikin Gida Da Ƙasashen Waje Karatun Digiri Na Biyu, Sun Yi Taron Nuna Godiya

    Daga Ibrahim Muhammad Ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala da za su tafi karatu manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan da gwamnatiin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe