Daga Ibrahim Muhammad Kano
An yi bukin buɗe katafaren rukunin shagunan zamani na TROPICAL MALL da kamfanin MC DREAM CONCEPT ya gina a harabar filin tsohon otel ɗin ROYAL TROPICANA a jihar Kano.
Bukin buɗe shugaban na TROPICANA MALL da aka gudanar a safiyar ranar Talata ya sami halartar ‘yan kasuwa da dama da suka yi fatan alheri da yabawa waɗanda suka samar da kasuwar.
Kwamishinan kasuwanci na jihar kano, Gwani Shehu Wada Gagagi, ɗaya daga manyan baƙi a taron a yin jawabinsa ya nuna damuwa a kan yadda ‘yan kasuwa masu kamfanoni ba sa jajircewa wajen ɗorewar masana’antunsu.
Ya yi nuni da cewa a wasu wuraren ana kafa kamfanoni kuma su kashe shekaru masu yawa suna ayyuka, sun wanzuwa tun daga kakanni da iyaye da ‘ya’ya da jikoki, su shafe shekaru masu yawa ba tare da tsayawa ba.
Sagagi ya ce suna shirin kiran taro na yin bita da zai ƙunshi ‘yan kasuwa da masu kamfanoni don tattauna yadda za a sami kafa masana’antu da yadda za su ɗore ana tafiyar da su ba tare da gazawa ba.
Kwamishinan ya yi fatan alheri da gina shagunan na TROPICANA MALL.
Ya ce kuma gwamnatin jihar za ta cigaba da bayar da goyon baya da zai bunƙasa kasuwanci a jihar Kano.
Da yake hira da ‘yan jarida, shugaban kamfanin MC DREAM CONCEPT da suka gina shugaban TROPICANA MALL, Injiniya Dakta Isma’ila Zubair, ya bayyana matuƙar jin daɗinsa bisa kammala ginin cikin nasara har aka zo ranar da ake buɗewa.
Ya yi nuni da cewa ba ƙaramin abu ba ne ka zo ka sa abu a gaba Allah ya taimaka ka fara ka gama lafiya babu wata matsala, babu wanda ya yi rauni a yayin aikin ginin, ko aka sami wani abu mara daɗi. Ya yi wa Allah godiya sosai.
Injiniya Zubair ya ce ginin TROPICANA MALL da aka buɗe yana da shaguna 624 da manyan shaguna Mall guda biyu da wajen sayar da abinci da Banki da masallaci da kuma ‘yan tebura saboda ƙananan ‘yan kasuwa.
Ya ce tun soma ginin sun bi ƙa’idodi na samun amincewar gwamnati har suka kammala aikin sun sami goyon bayanta.
Shugaban kamfanin na MC DREAM CONCEPT, Injiniya Isma’il Zubair ya ce an soma aikin ginin ne a watan Janairu 2022, aka buɗe aka gama 30 ga Satumba 2025 da tun fari an tsara kammala ginin ne a cikin watanni 18, amma saboda yanayin yadda aka sami kai a ƙasar nan na hauhawar farashin kaya da ya shafi kayan gini ma sai aka sami tsaiko har sai wannan lokaci.
Ya yi kira ga ‘yan kasuwa su kalli abin da MC Dream Concept ta yi na gina Tropicana Mall tsarin ginin ko ana ruwa ba za a sami cabi ba, sun sanya kayan kashe gobara da gaggawa za su kuma sanya kayan sadarwar zamani da internet mai ƙarfi.
Injiniya Dakta Isma’il Zubair ya yi nuni da ƙalubalen da suka fuskanta shi ne na lokacin da suka soma aikin, wasu mutane ba su yarda da su ba, suna kallon su a matsayin kamar ‘yan damfara ne, wasu na ginin tamkar guduwa za a yi da kuɗin mutane, kuma ga shi cikin ikon Allah sun fara har an gama cikin gaskiya da riƙon amana.
Dakta Isma’il yace MC Dream Concept na da matasa da ke aiki a ƙarƙashinsa, don haka kiran su ga jama’a da suke da tsofaffin wurare da ba su san yadda za su gina a zamanance ba, su tuntuɓe su a ofisoshinsu na Kano ko Abuja ko na Lakoja za su zo su duba su ga yadda za su haɗa kai a ga abin da za a yi da zai bunƙasa cigaban kasuwanci a wurin.






