An Yi Kira Ga Al’ummar Rano Kan Jajircewa A Kan Neman Ilimi Da Yin Sana’o’i Na Dogaro Da Kai

Daga Ibrahim Muhammad

Kwamishinan Ma’aikatar Raya Al’adu da Yawon Buɗe Ido na jihar Kano, Hajiya A’isha Lawan Saje Rano da Hajiya Sa’adatu Ada’ Isah mafaka iya a Jami’ar Yusuf Maitana na daga cikin mata ‘yan asalin ƙaramar hukumar Rano da ƙungiyar RAKIBU ta karrama a taron da ta gudanar a garin Rano ranar Asabar.

Da take zantawa da ‘yan jarida bayan karrama ta, Hajiya A’isha Lawan Saje Rano ta bayyana farin cikinta bisa haɗa wannan taro don karrama su da yaba musu da yaba wa gwamnati bisa ɗauko ‘yar cikinsu dabara wannan muƙami da suke ganin su a yanzu kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Ta ce al’umma shaida ne a kan irin manyan mutane da suka halarci taron masu muƙamai na jihar Kano da ma waɗanda ke da muƙamai a matsayin ƙasa ‘yan asalin ƙaramar hukumar Rano da aka ba su lambar girmamawa.

Ta yi nuni da cewa irin wannan abin sone da ya kamata duk sauran ƙananan hukumomi a ce suna da makamantan irin wannan ƙungiyar ta kishin yanki da za ta taimaki mutanenta da kuma ƙarfafa waɗanda Allah ya bai wa wata dama, domin ta haka ne za su je su nemo abin da zai ƙara kawowa yankin cigaba, ta haka za su taimaki na ƙasa da irin wannan haɗin kan.

Ta gode wa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya ɗauko wannan dama ya ba ta a farko a Ma’aikatar Mata da yara da masu buƙata ta musamman a yanzu ma ya sake ba ta wannan dama a Ma’aikatar Raya Al’ad da buɗe ido, kuma al’umma shaida ne a kan irin ayyuka na cigaba da Gwamna ke bijirowa da shi a jihar Kano da kuma alkhairi da al’ummar Kano ke amfana.

Ta ce duk inda aka ambaci Rano ita za a soma kawowa, ita kanta Saje nan ta fito ne daga irin jajircewar magabatan su waɗanda suka zauna suka fito da muryar da ta haɗin kai, suka nuna kishin yankunansu, wanda kuma sune suka reni wannan ƙungiya da yanzu ta RAƘIBU su ma yanzu sun zo suna ƙara ɗorawa a kan abubuwan magabata.

Hajiya A’isha Lawan Saje Rano ta ce ba abin mamakin bane a duk inda aka faɗi sunan Rano a cikin ƙasar nan ne da a ƙasashen duniya za su tabbatar sun amsa sunan, kuma suna ne mai kyau da nagarta.

Suna fata Allah ya ƙara wuce musu gaba ya ba su damammaki da za su cigaba da taimakon yankinsu da jihar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.

Ita ma ɗaya daga cikin muhimman mata da aka karrama a taron Hajiya Sa’adatu Ada’u Isah wacce ma’aikaciya a Jami’ar Yusuf Maitama Yusuf Kano, kuma mai gudanar da sana’o’i na dogaro da kai ta ce wannan karramawar abin farin ciki ne domin zuwan ta taron ma kawai ta kalli ɗimbin mutane da suka taru a Rano ba abin da za ta ce sai godiya ga Allah.

Ta yi nuni da cewa duk inda aka shiga a faɗin ƙasar nan har ƙetare idan ka ce Rano a cikin kowane harkoki sai an sami wani daga wannan yankin da ya shahara har ya kai wannan suna inda ya kai. Don haka ta ja hankalin al’ummar ƙaramar hukumar Rano su ƙara dagewa kamar yadda aka san su wajen jajircewa, su yi karatu su yi ilimi da cigaba da yin sana’o’i na dogaro da kai domin sune suka kai su ga gaci da suka yi fice.

Hajiya Sa’adatu Ada’u Isah ta ƙara da cewa al’ummar Rano musamman matasa su jajirce su tsaya su yi amfani da lokacinsu da lafiya da Allah ya ba su da ƙuruciya wajen ganin sun gina kan su ta yin karatu da kuma sana’a na dogaro da kai ta kuma gode wa ƙungiyar kishin cigaban Rano, Kibiya, Bunkure bisa karramawar da hakan zai ƙara musu ƙaimi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum