An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

Daga Ibrahim Muhammad

An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.

Taron ya sami halartar Sanatan Kano ta Tsakiya, Hon. Rufa’i Sani Hanga; Kwamishinan Kasuwanci na Jihar Kano, Wada Sagagi; wakilai daga masarautun Kano, da shugabannin cibiyoyin kasuwanci daga Kaduna, Zamfara, Gombe da sauran jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa.

Da yake jawabi yayin rufe baje kolin, Ambasada Usman Darma ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da taron cikin kwanciyar hankali tun daga buɗe shi har zuwa kammalawa.

Ya tunatar da cewa an kafa cibiyar kasuwanci ta Kano tun shekarar 1922, kuma an fara shirya baje koli na farko a 1979, wanda ya kai wannan biki zuwa karo na 46.

Shugaban ya gode wa gwamnatin Jihar Kano bisa muhimman ayyukan da ta aiwatar wajen inganta kasuwanci, yana mai cewa cibiyar tana da shirin ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnati don bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Ya ce daga cikin nasarorin bana har da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ‘yan kasuwa daga Ruwanda da Ghana, da tattaunawa da jakadun Bangladesh, Indiya da Sin kan zuba jari a fannonin wutar lantarki, kimiyya, fasaha da masana’antu.

Darma ya ce sun tattauna da hukumar NIMASA kan hanyoyin bunƙasa kasuwanci ta ruwa, tare da karɓar wakilai daga jihohi da dama, musamman Filato da Zamfara, waɗanda suka nuna sha’awar faɗaɗa hulɗar kasuwanci da Kano. Haka kuma, a karo na farko, an gudanar da gasar fasaha ga matasa, inda wani matashi mai buƙata ta musamman, Malam Ibrahim Abubakar, ya nuna fasahar kera mota. Ya lashe gasar, cibiyar ta ba shi tallafin ₦1,000,000.

Shugaban KACCIMA ya ce cibiyar na shirin kafa Bankin Microfinance don tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, tare da gina cibiyar horas da fasaha ta zamani don bunƙasa sana’o’i da inganta arziƙi.

A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Cibiyar Kasuwanci ta Gombe, Hon. Jalo Ahmad Ganga (Sarkin Tafarkin Gombe), ya ce Kano ita ce cibiyar kasuwanci a Nijeriya, kuma jihohin su kan yi koyi da ita.

Ya ce sun koyi abubuwa da dama a wannan baje koli da za su koma su aiwatar a jiharsu, tare da ƙara ƙarfafa hulɗa da cibiyar kasuwanci ta Kano.

Shugaban Cibiyar Kasuwanci ta Kaduna, Alhaji Faruk Faruk Sulaiman (Pasman), wanda ya daɗe da shiryawa halartar Ranar Dangote, ya ce karamcin da ya gani daga abokinsa Ambasada Darma ya sa ya zauna har zuwa rufe taron. Ya yaba da yadda aka bai wa ƙananan ‘yan kasuwa dama, yana mai cewa Kaduna za ta shirya nata baje kolin mai tsawon kwanaki 10 a baɗi, sannan ta bi shi da baje na kayan abinci don rage tsadar kayan masarufi ga al’umma.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Kaduna ƙarƙashin Sanata Uba Sani ta gudanar da manyan ayyuka, kuma a matsayinsa na sabon shugaba, ya ƙuduri niyyar ganin an inganta rayuwar ‘yan kasuwa da abokan hulɗarsu.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Daga Ibrahim Muhammad Shugabar hukumar taimakekeniyar kula da lafiya ta jihar Kano, Dakta Rahila Aliyu Muktar ta bayyana godiya ga Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa sahale musu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe