Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya rantsar da AVM Ibrahim Umar mai ritaya a matsayin sabon Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida.
Gwamnan ya yi kira ga sabon Kwamishinan ya gudanar da aikinsa bisa a kan gaskiya da riƙon amana don samar da cigaban jihar Kano.
Kwamishinan Sharia na jihar Kano, Barrista Haruna Isa Dederi shi ne ya jagoranci rantsuwar a yayin zaman Majalisar Zartaswar karo na 28 da ya gudana a sabon gidan gwamnati da ke rukunin gidajen Kwankwasiyya.






