Ba Ma Buƙatar Sulhu Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje -APC

Daga Ibrahim Muhammad

Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta ce ya fahimci ƙoƙarin da Kwankwaso yake na shigowa cikinta ne ya sa Abdulmumin Jibrin Kofa ya fara kiraye-kirayen a sami sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

“Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Kofa ya zo da ita, yaudara ce. A siyasance ba ma buƙatar yin siyasa tare da Kwankwaso”.

Kakakin jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya ya yi da wani gidan radio da ke Kano.

Ya ce, “So suke su dawo APC don su ƙwace ta daga wajenmu. Domin Kwankwaso ya saba yin hakan tun da ya yi wa Malam Ibrahim Shekarau da dole sai da muka bar masa APC muka koma PDP. Haka kuma ya sake yi musu a PDP. Don haka mun gano wayon.

“Idan da gaske ne, Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya kamata ya daidaita Kwankwaso da Ganduje, amma ba Kofa ba.

“Idan ka lura da yadda Kofa ya zayyano muƙaman da Kwankwaso ya riƙe da waɗanda Ganduje ya riƙe za ka gane shi (Kofa) ya yi kaɗan ya ce zai sulhunta Kwankwaso da Ganduje,” in ji Aruwa.

Don haka ya ce su ba sa buƙatar yin sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje saboda daga ƙarshe cewa za a yi a haɗe, kuma in an haɗe su za a cutar.

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa a ƙarshen makon da muke bankwana da shi ya ce ya zama wajibi a sulhunta Ganduje da Kwankwaso saboda cigaban jihar Kano.

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe