Daga Ibrahim Muhammad
Jigo a siyasar yankin Sumaila da ke kudancin jihar Kano, Hon. Bello Musa ya bayyana cewa yanayin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf take masu kyau da inganci, ba za a kwatanta da gwamnatin APC ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba.
A lokacin da yake zantawar da manema labarai a Kano, Hon. Bello Musa ya, “Har ga Allah muna ganin bambanci sosai a wannan gwamnatin idan aka kwatanta ta da ta baya. Ayyuka ga su nan ana ta yi i babu dare, ba rana a ko’ina ga hanyoyi ta ko’i’na,” ya tabbatar.
Alhaji Bello Musa Sumaila ya ce a yankinsu ƙaramar hukumar Sumaila ana yin hanyoyi da gyara makarantu, “In ka ga yadda aka gyara wata makarantar Firamare da ta shekara 90 ba za ka ce tsohuwa ba ce da kuma ayyuka na samar da ruwa da abubuwa da dama” ya bayyana.

Hon. Bello Musa Sumaila ya bayyana dalilinsa na shigowa Kano da cewa, “Mun zo ɗaurin aure ‘ya’yan mai bai Gwamnan rashawa kan siyasa, kuma taro ya yi taro, Allah ya ba da zaman lafiya, kuma ƙauna ce ta tara al’umma ba kuɗi aka bai wa kowa ba.
An bayyana mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara na musamman da cewa mutum ne na kowa mai faɗa da cikawa, shi ya sa ake ce masa Kotun Ƙoli saboda yana yanke hukunci a kan gaskiya, kuma haka yake, shi ya sa mutane ke ganin kamarsa.
Ya ce shi al’amarin aure zama ne na haƙuri da juna. “Hausawa na cewa, zo mu zauna ne, zo mu saɓa. Ba ma kamar wannan zamani da kowa kusan zuciyarsa a kusa take, amma duk in aka yi haƙuri sai a zauna lafiya,” in ji shi.








