Babbar Sallah: Gwamna Lawal Ya Buƙaci Musulmin Zamfara Su Tuna Da Muhimmancin Sadaukarwa Da Halin Ƙwarai

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya taya al’ummar Musulmin Zamfara da Nijeriya murnar zagayowar ranar Babbar Sallah ta bana.

Musulmi a faɗin duniya na murnar ranar Babbar Sallah, wanda kuma aka fi sani da ‘sallar layya,’ yau Juma’a, 6 ga watan Yuni 2025.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa bikin Babbar Sallah na ɗaya daga cikin bukukuwan addini mafi girma a kalandar Musulunci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana ta Babbar Sallar.

“Babbar Sallah tana bai wa Musulmi damar girmama sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi na ɗansa domin biyayya ga umarnin Allah.

“Tana tunatar da mu muhimmancin imani, rashin son kai, da sadaukarwar da muke da ita ga al’umma da bil’adama, ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani a kan kimar sadaukarwa da biyayya ga Allah Maɗaukakin Sarki.

“Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da duk wani nau’i na munanan ɗabi’u da kuma laifuka da suka shafi al’ummarmu.

“Haƙƙinmu ne na gamayya mu yi aiki don tabbatar da tsaron al’ummarmu, jiharmu da Nijeriya baki ɗaya.

“Allah ya karbi sadaukarwarmu a matsayin ibada, Allah ya albarkaci jihar Zamfara da ƙasar mu Nijeriya.”

Related Posts

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal