Yadda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Bai Wa Mai Sayar Da Jarida Kyautar Kujerar Makkah

Daga Ibrahim Muhammad

Malam Muhammad Lawan Kiru, wani mai sayar da jarida, ya gode wa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf saboda ba shi kyautar kujerar Hajji da ya tafi bana.

Ya bayyana wannan abin alkhari ne da Gwamnan ya yi masa ga tawagar manema labarai a birnin Makkah a cewa, jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, Suleman Dederi.

Ya ce mai sayar da jaridar ya bayyana wa manema labarai cewa ya saba da Gwamna Abba Kabir Yusuf ne a dalilin sayen jarida da yake yi a hannunsa a birnin Abuja shekaru 30 da suka gabata.

Ya ƙara da cewa, Gwamna Abba ya tuna da shi ne bayan wani ya zo wajen sa sayen jarida, suka tattauna a kan Gwamnan, shi ne ya kai wa Gwamnan labarinsa, take kuwa Gwamnan ya tuna da shi har ma ya ba shi kyautar kujerar Hajji domin ya sauke farali.

Malam Muhammad Lawan Ƙiru, wanda ya ce mafarkinsa ya zama gaskiya, ta yi godiya Gwamna Abba Kabir Yusuf da wannan dama da bai samun kamar ta ba a rayuwarsa.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum