Cibiyar Markazi Isalil lkhair Li Ummati Muhammad Ta Yaye Ɗaliban Da Suka Koyi Sana’o’i

Daga Ibrahim Muhammad

Mataimakin babban Kwamandan Hukumar Hisba na jihar Kano, Sheikh Aminudeen Mujahideen Abubakar ya ja hankalin mata da matasa su dage wajen neman ilimin rayuwa da na addini da na sana’o’i da na dogaro da kai.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron ya ye ɗalibai mata na ɓangaren koyon sana’o na Cibiyar Markazi Isalil lkhair Li Ummati Muhammad da aka gudanar a harabar makarantar fako.

Sheikh Aminudeen Mujahideen ya yaba wa Malam Aminu Alkasim, wanda shi ne ya assasa Cibiyar bisa wannan kyakkyawan aiki da yake me cike da lada ya fatan al’ummar yankin da iyaye da masu hali za su cigaba da bai wa Cibiyar gudummawa don cigaba da samun nasarar cigaba da nganta tarbiyya da ba da ilimi da horon a kan sana’o’i da take.

Shi ma a nasa jawabin, ɗaya daga cikin manyan baki a taron, Dakta Nura Salihu Adam da aka fi sani da Salihudeen ya ja hankalin iyaye mata ne a kan muhimmancin yin sana’a, wanda zai taimaka wajen maganin duk wata damuwa.

Ya yi nuni da cewa ita sana’a magani ce ta masifar yunwa domin idan kana da ita da ita za ka ci ka sha ka magance yunwa, ya yi kuma bayanai da kafa misalai da dama a kan muhimmancin riƙe sana’o’i na dogaro da kai ga mata da matasa.

Salihudeen ya yaba matuƙa da irin sadaukarwa da Malam Aminu Alƙasim yake wajen ganin ya kyautata tarbiyyar al’umma ta koyar da tarbiyya da ilimin addini da na sana’o’i da yake.

Ya yi kira ga iyaye su cigaba da ba shi haɗin kai da goyon baya.

Shi ma a nasa ɓangaren ko’odineta na Markazi Isalil lkhair Li Ummati Muhammad, Malam Aminu Alƙasim ya gode wa dukkan manyan baƙi da suka halarci taron na bai wa ɗalibai da suka koyi sana’o’i shaida.

Ya ce bambancin taron ba na da wanda aka yi a baya shi ne halartar kusan duka manyan baƙi da suka gayyata musamman mataimakin shugaban Hisba da Malam Bashir Ɗantani da Salihudeen da Darakta mai kula da sashen ilimin manya Binta Abubakar da ‘yan’uwa da iyayen hakan ya ƙara musu ƙarfin gwiwa da cigaba da jajicewa.

Ya ce waɗanda suka amfana a koyon sana’o’i a wannan karon su 11 ne, amma waɗanda suka kammala aka ba su shaida su huɗu ne, kuma abubuwa da suka koya sun haɗa da zannuwan gado, bulawus, haɗa man shafawa da abubuwan kansa.

Malam Aminu Alƙasim ya yi kira ga Hukuma da masu hannu da shuni su shigo cikin lamarin, domin abu ne da ake raya al’umma duk abin da za ka koya wa mutum na ilimi da sana’a da tarbiyya.

Ya ce ya kamata a ce ka raya shi ka ba shi madafa zai ji daɗi idan gwamnati da masu hannu da shuni sun ba da gudunmawa abu zai kyau sosai.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe