Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan goma sha Biyar (15 Billion Naira)

A wani mataki na rage radadin talauci a tsakanin al’umma, gidauniyyar Dangote ta kaddamar da tallafin rabon abinci na kasa a jihohin kasar nan inda mutane miliyan daya suka amfana.

Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa tallafin zai game dukkanin kananan hukumomin kasar nan 774, na kimanin buhunan shinkafa milyan daya me nauyin kilo 10.

Jihar Kano ta samu kaso mafi girma inda mutane 120,000 suka amfana wanda daga bi sani rabon zai ci gaba a sauran jihohin kasar nan.

Haka zalika rabon shinkafa mai kilo 10 zai ci gaba a dukkanin sauran kananan hukumomi na Jihar Kano.

Bikin kaddamar da rabon abincin dai ya gudana ne a budadden dakin taro na fadar Gwamnatin Kano da shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta da kuma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A cewar Alhaji Aliko Dangote , sun ga dacewar raba kayan abincin ne ba wai kawai don magance matsalar yunwa ba, har da batun saukakawa al’umma wajen gudanar da rayuwa a kasa ba-ki daya.

“Hakan kuwa ya zama wajibi duba da muhimmancin zumunci da ‘yan uwan taka dake tsakanin mu, da kuma hadin kai a wannan lokaci da ake fusakantar kalubalen rayuwa.

“A wannan wata na Ramadan, lokaci ne da muke sadar da halayen nagarta, wanda ke taimakawa wajen tallafawa al’umma”.

“Ina da kwarin gwuiwar sanar daku cewa wannan tallafin na yanzu na musamman ne, duk da cewar mun yi irin sa a kasa da wata guda da ya gabata, amman muka ga dacewar sake tallafawa al’umma musamman a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.

Attajirin Alhaji Aliko Dangote, ya shaidawa gangamin taron al’ummar cewa wannan kari ne akan tallafin da ya gudana na mutane dubu goma da ake ciyarwa kullum a Jihar Kano, yace Tallafin shinksfar Mai kilo goma da ya kaddamar kimanin miliyan Daya wanda ya lakume kudade Naira bilyan 15 a kasa ba-ki daya.

Da yake jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shirin rabon tallafin kayan abincin inda yace yazo a dai-dai lokacin da dimbin al’umma ke bukatar hakan.

Gwamnan ya bukaci kwamitin da aka dorawa nauyin rabon kayan abincin ciki har da hukumar HISBAH ta jiha da su maida hankali wajen aiwatar da aikin cikin gaskiya da rikon amana don cimma manufar shirin.

“Wannan shirin zai taimaka wajen rage saukaka rayuwa, a cewar Gwamnan Kano.

“Inda ya sake kara jinjina kaso mafi tsoka da jihar ta samu”.

Zouera Yousoufou dake zaman shugaban gidauniyyar ta Aliko Dangote tayi karin haske kan kokarin Alhaji Aliko Dangote wajen tallafawa al’umma, inda yace shakka babu gidauniyyar zata ci gaba da baiwa wannan bangaren muhimmanci.

“Mune a gidauniyyar Dangote muke ganin ya zama wajibi a sanar da al’umma irin kokarin da yake yi don sauran al’umma masu kudi su kwaikwayi halayensa na gari na tallafawa al’umma”, a cewar Yousoufou

Rabon tallafin kayan abincin da Alhaji Aliko Dangote ya jagoranta na shinkafa miliyan Daya dake dauke da kilo goma na nuni da kokarin shi wajen rage radadin rayuwa da marasa galihu ke fuskanta da kuma kara dankon zumunci a tsakanin al’umma.

Related Posts

Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

Daga Ibrahim Muhammad Mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara ta musamman kan harkokin Majalisar Dokoki, Rt. Hon. Isyaku Ali Ɗanja, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba…

Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano