Dangote ya rage farashin man fetur a Najeriya

Kamfanin mai na Dangote ya bayyana yi wa ‘yan kasuwa da ke saro man fetur a matatarsa ragin kuɗin man.

Cikin wata sanarwa da babban jami’in sadarwar kamfanin, Anthony Chiejina ya fitar ranar Lahadi ta ce an rage wa ‘yan kasuwar farashin da suke saro man daga naira 990 zuwa naira 970, domin ”nuna godiyarsa ga ‘yan Najeriya”.”

A yayin da shekarar nan ke zuwa ƙarshe, wannan ita ce hanyar da za mu gode wa mutanen Najeriya kan irin goyon bayan da suka riƙa nuna mana har matatarmu ta tabbata. Wannan ƙari ne kan godiyar da muke yi wa gwamnati bisa goyon bayan da ta ba mu wajen ɗaukar matakan da suƙa ƙarfafa wa kamfanonin cikin gida gwiwa”.

Sanarwar ta ƙara da cewa matatar ba za ta yi wani abu da zai rage ingancin man da take tacewa ba, wanda ta ce ingantacce ne da ba ya gurɓata muhalli.

Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki da matatar ta fara fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje domin sayarwa

Related Posts

Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

Gwamnatin Kano da Majalisa na Tafiya Lafiya Babu Saɓani -Isyaku Ali Danja

Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano