Daga Ibrahim Muhammad
Babu abin da za mu ce sai godiya ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf bisa kulawa da take da al’amuran al’ummarta, wanda duk abin da ya taso ba ta gudanar da shi kai tsaye sai ta yi tuntuɓa ta ji ra’ayin al’umma.
Jagoran Kwankwasiyya na mazabar Gama jigo a jam’iyyar NNPP a jihar Kano ne ya bayyana hakan.
Ya ce cikin kuɗure-kuɗure da ake buƙatar kawo gyara a ciki na tsarin mulkin ƙasa, wasu daga ‘yan majalisunmu a Gwamnatin Tarayyar sun shigar da buƙatun irin waɗannan abubuwa da ake don gyara, don haka jihar Kano tana kan gaba wajen gudanar da gyare-gyare da ake so a yi na kundin tsarin mulki.
Hon. Muhammad Adamu Bomboy ya ce suna goyon bayan gwamnatin Kano da al’ummarta kan neman ƙarin jiha da ƙananan hukumomi, kwamiti da gwamnati sun kalli wannan buƙata.
Kuma in aka duba ɓangaren tsaro ya shiga wani yanayi, don haka ake so a sahale kowace jiha ta yi domin za su kawo gudunmawa ga inganta tsaro.
Ya ƙara da cewa idan aka yi ƙarin ƙananan hukumomi da ƙirƙirar jiha daga cikin Kano zai taimaka wajen kusanto da gwamnati kusa da al’umma, in aka duba akwai adadin yanki da yawan mutane da ya kamata a ce sun zama ƙaramar hukuma, amma sai ka ga wani Kansila a wani yankin ya fi ma wata ƙaramar hukumar, amma in aka samu ƙarin ƙananan hukumomi za a matso da gwamnati kusa da al’umma.
Hon. Bomboy ya ce tun zuwan wannan gwamnati ta Abba Kabir Yusuf tana gudanar da duk wani abu da ya shafi al’umma babu zancen bambancin siyasa kan irin ayyuka da ake na raya ƙasa da kuma yadda ake sauraren koke-koke na al’umma, kuma ana gudanar da gwamnati a buɗe, babu bambanci na ra’ayin jam’iyya ta janyo kowa, kuma ayyukanta ido na gani hannu ya taɓa ƙafa ta taka.








