Daga Ibrahim Muhammad
Ɗan kasuwa kuma shugaban rukunin kamfanonin HAMIR, Alhaji Hamisu Rabi’u Jingau, ya nuna mutuƙar alhininsa bisa rasuwar Galadiman Kano babban ɗan majalisar masarautar Kano, Alhaji Abbas Sanusi da ya rasu ranar Talata.
Ya yi nuni da cewa an yi rashi na jagora da kullum yake ƙoƙarin haɗa kan al’umma da nusar da su muhimmancin zaman lafiya gare su.
Alhaji Hamisu Rabi’u, wanda ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya gidan marigayin
ya ce, a matsayinsu na masu tasowa za su cigaba da koyi da halaye managarta na irin waɗannan magabata da suka bayar da gunmuwa wajen haɗin kan al’umma da mutuntawa.
Shi ma a yayin ta’aziyyar, shugaban kamfanin taki na ALYUMA, Alhaji Ali Maitaki ya ce, rashin Galadiman Kano Alhaji Abbas, rashi ne babba mai wahalar cikewa, musamman idan aka yi la’akari da irin gudunmuwa da suka bayar ga cigaban al’umma.
Alhaji Ali Maitaki ya ce, za a cigaba da tuna marigayi Galadima da irin gudunmuwa da ya bayar, su kuma al’umma da iyalansa za su yi haƙuri da wannan rashi da aka yi.






