Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaɓen Fidda Gwanin PDP Na Gwamnan Edo

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jagoranci zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar PDP a zaɓen Gwamnan jihar Edo da ke tafe.

A zaɓen da ya gudana yau Alhamis ɗin nan a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke garin Benin, Asue Ighodalo ne ya zama zakara, wanda ke nuni da cewa shi ne zai yi wa jam’iyyar takara a matakin Gwamnan jihar ta Edo.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Abuja, ya bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin tsari da kwanciyar hankali, inda aka zaɓi wanda zai yi wa jam’iyyar PDP takara a zaɓen Gwamnan da ke tafe cikin watan Satumba mai zuwa.

Tun farko a jawabin sa kafin a fara zaɓen, Gwamna Dauda Lawal ya hori ‘yan takarar da su yi amanna da tsarin zaɓen, inda ya ba su tabbacin za a gudanar da zaɓe mai cike da adalci.

“Ko yanzu za ku iya gani, an yi tsari mai kyau buɗaɗɗe. Za mu gudanar da zaɓe na gaskiya mai inganci don samar da ɗan takara ga jam’iyyar mu a jihar Edo.”

Sanarwar ta Malam Idris ta ce, bayan kammala zaɓe da ƙirgawa, Gwamna Dauda Lawal, a matsayin sa na Baturen zaɓe, sai ya bayyana Ighodalo a matsayin gwanin da aka fitar. Inda Gwamnan ya bayyana cewa Ighodalo ya samu ƙuri’u 577, wanda ya doke sauran ‘yan takarar su tara.

“A matsayi na na jagoran gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP, na bayyana Asuelimen Ighodalo a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 577.

“Ina taya shi murna, tare da yin kira ga sauran ‘yan takarar da su karɓi wannan sakamako da zuciya ɗaya. Wajibin mu ne mu haɗa kai mu dumfari yaƙi na gaba, zaɓen Gwamna.

“Wajibin mu ne mu sanya buƙatun jam’iyya birbishin buƙatun mu. Yanzu muna da ɗan takara, dolen mu mu bayar da cikakken goyon bayan mu.

Related Posts

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal