Gwamna Lawal Ya Jagoranci Taron Majalisar Zartarwa, Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaƙi da matsalolin tsaro a jihar aiki ne na haɗin kai da ya rataya a wuyan kowa da kowa, ba na gwamnati kaɗai ba.

A ranar Litinin, gwamnan ya jagoranci zama na 18 na Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara a Gidan Gwamnati da ke Gusau, inda aka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro, ilimi, kiwon lafiya da kuma ci gaban gine-gine a faɗun jihar.

A jawabin buɗe taron, Gwamna Lawal ya ce, “Ina so na tunatar da mu duka cewa yaƙin da muke yi da rashin tsaro babban nauyi ne na haɗin kai. Mun samu nasarori da dama, inda muka farfaɗo da zaman lafiya a yawancin yankuna na jihar. A yau, barazanar ’yan bindiga ta ragu matuƙa idan aka kwatanta da shekarun baya.”

Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su kasance masu aiki da faɗakarwa, su kasance kusa da jama’ar yankunansu da kuma shugabannin ƙananan hukumomi. Ya umarce su da su riƙa isar da rahotanni na yau da kullum ga Kwamishinan Tsaro, tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare al’umma da zaunar da zaman lafiya a jihar.

Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙarfafa mambobin majalisar su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da ingantacciyar tafiyar da al’amuran mulki da gudanar da ayyukan ci gaba cikin nasara.

Sulaiman Bala Idris
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
20 ga Oktoba, 2025

Related Posts

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe