Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a ƙoƙarinsa na kyautata dagantaka tsakanin manoma da makiyaya ya bayar da dama ga dukkanin shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano su taimaki Fulani a kan Labi da makiyaya don kyautata sha’anin rayuwar Fulani.
Babbar mataimakiya ta musamman ga Gwamnan Kano a kan Fulfulde Hajiya Ruƙayya Umar Gadon Ƙaya ce ta bayyana hakan a taron ƙungiyar Sulluɓawa da aka yi a Kano ta ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya tsaf yana da kyawawan ƙudure-ƙudure domin bunƙasa cigaban Fulani da za a gan su a aikace ana aiwatarwa.
Ta ce yanzu haka lura da yadda Fulani ke shan wahala a zuwa aikin Hajji ya shirya ɗaukar malamai da za su riƙa yin amfani da harshen Filatanci su jagoranci Fulani wajen aiwatar da ibadar aikin Hajji.
Sannan zai ɗauki ‘ya’yan Fulani waɗanda suka san harkar lafiya su riƙa yi wa Fulani magani. “Duk irin waɗannan tsare-tsare da yawa suna nan tafe”, in ji ta.
Hajiya Ruƙayya Umar Gadon Ƙaya ta ja hankalin Fulani musamman makiyaya da manoma da cewa su sani abin da ya yi manomi shi ne ya yi makiyayi, tsakaninsu tamkar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. “Domin mai kiwon shanu yana noma ya ci abinci, manomi shi ma yana buƙata daga makiyaya. Akwai auratayya a tsakaninsu. Ya kamata a yi wa juna adalci,” ta jaddada.
Ta ce kada Fulani su riƙa tura yara ƙanana suna yi wa manoma ɓarna a gonaki, su tura masu hankali. Su ma manoma in suka kwashe abin da suka noma sai su bar wa makiyaya su ɗan kalaci abincin shanu kada a riƙa bin su da sara da duka har a tunzura su abu ya riƙa zama rigima a tsakani. Hakan ba daidai ba ne, domin zaman lafiya ya fi komai a rayuwa.
Hajiya Ruƙayya Umar Gadon Ƙaya Babbar mataimakiya ta musamman ga Gwamnan jihar Kano a kan Fulfude ta yi fatan Allah ya haßa kan Fulani da manoma, kuma su gujewa fushi da ɗaukar doka a hannu. “Duk abin da ya taso a je ga hukuma da aka tanade ta domin ƙwatowa kowa ‘yancinsa, kuma duk abin da ya taso a kai ga magabata don ɗaukar mataki,” ta ƙarkare.






