Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa duk wani mataki da ya kamata a dauka na gyara ilimi Gwamna jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zuwan sa ya na dauka sakamakon ya zo ya sami fannin a ragargaje da sai an yi da gaske.
Allah ya kawo shi yasa harkar ci gaban ilimi a gaba fiye da komai ba don haka ba da ba a san yadda za a sami kai ba.
Babban Sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Kano.Alhaji Bashir Baffa Muhammad ne ya shaida hakan ga manema labarai ya kara da cewa yanzu a matsayinsu na ma’aikata su ya ragewa su rike masa amana, mutukar ilimin ya farfado matasa da ake ganinsu suna wasu abubuwa na rashin kyautawa za su daina su gina kyakkyawan ci gaban na rayuwa.
Ya ce Kwamishinan ilimi mai barin gado Haruna Doguwa ya yi rawar gani da kokari saboda mutum ne mai kaiwa da kawowa da son ayi tafiya tare da yake bada shawara a aiki da suka yi dashi tare ya gyara masa aiki, tunda ya tarad dashi a ma’aikatar.
Bashir Baffa ya ce a wajensa Umar Haruna ba tafiya ya yi ba tunda yana cikin Gwamnati kuma yana kaunar ci gaban ta da na jihar Kano kodayaushe suke bukatar shawarar sa zasu je wajensa ya basu.
Babban Sakataren na ma’aikatar ilimi na jihar Kano ya ce suna alfahari da sabon Kwamishina Ilimi da aka kawo musu Gwani Ali Haruna Makoda mutum ne akili mai jajircewa me aiki tukiru abu mafi girma Gwani ne na Qur’ani da yake da kishin jihar Kano da son ci gaba, mutum ne mai hada kan ma’aikata a tafi tare.
Bashir Baffa Muhammad ya ce za suyi aiki karkashinsa da ba shi hadin kai saboda suna da manufar ganin cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta cimma nasara a manufarta na gyaran ilimi da tasa a gaba.
A ranar Laraba ne dai Dokta Gwani Ali Haruna Makoxa ya fara aiki a matsayin sabon kwamishinan ilimi na jihar Kano a hukumance, inda ya yi alkawarin kara bullo da wasu shirye-shirye da nufin bunkasa fannin ilimi a jihar.






