Daga Ibrahim Muhammad
A wani salo na tabbatar da doka tare da kawo tsafta a ɓangaren ɗab’i, Hukumar tace finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-mustapha ta yi nasarar ganowa tare da kama wasu na’urori da ake amfani da su wajen buga hotunan batsa ga masu sana’ar maganin gargajiya a wasu unguwannin Jihar Kano.
Wannan na cikin wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman Jami’in yaɗa labarai na Hukumar ya raba wa manema labarai.
Kayayyakin da aka kama sun haɗa da kwamfutoci da kuma injunan buga hotuna.
Da yake holin kayan da Hukumar ta kama, Alhaji Abubakar Zakari Garun Babba Darakan Dab’i na hukumar ya bayyana wuraren da aka kama waɗannan kayayyakin da suka haɗa da wasu unguwanni a ƙaramar Hukumar Birni da wasu ƙauyuka a ƙaramar Hukumar Wudil.
Garun Babba ya nuna taikacinsa kan yadda wasu ke fakewa da sana’ar buga takardu suke buga hotunan batsa.
Ya yi gargaɗin cewa Hukumar ba za ta lamunci hakan ya cigaba da faruwa a faɗin Jihar Kano ba.
Hukumar na cigaba da riƙe kayan inda take dakon shawarar lauyoyinta domin ɗaukar mataki na gaba.
Garun Babba ya gargaɗi masu sana’ar buga takardu da su shiga taitayinsu domin gujewa fushin doka. Ya yi kira ga al’umma da jami’an tsaro a kan su cigaba da bai wa Hukumar cikakken goyan baya da haɗin kai, domin samun nasarar kawo ƙarshen irin waɗannan ayyukan a faɗin jihar Kano.






