Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban Cibiyar Masana’antu, Ma’adinai da Ayyukan Gona ta Jihar Zamfara, Dakta Hassan Buhari Tafidan Maradun, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Dakta Dauda Lawan Dare na ci gaba da ɗaukar matakai domin farfaɗo da harkokin kasuwanci, masana’antu da ma’adanai a faɗin jihar.

Dakta Buhari ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da ’yan jarida a Kano, bayan kammala bikin Special Day na Jihar Zamfara a bikin baje koli na duniya karo na 46 da ake gudanarwa a Kano.

Ya ce tun kafin gano ma’adinan man fetur, auduga da gyaɗa ne suka fi kawo kuɗaɗen shiga a ƙasar nan, kuma Zamfara na daga cikin jihohin da suka daɗe suna taka muhimmiyar rawa a harkar noman auduga.

Saboda noman auduga da ake yi a Zamfara, har ana gasa tsakaninta da Katsina wajen yawan amfanin da ake samu. A faɗin ƙasar nan kuwa Zamfara ce ta fi yawan masana’antar sarrafa auduga,” in ji shi.

Tafidan Maradun ya ce ko da yake noman auduga ya ɗan ja baya a wasu lokuta, an fara ɗaukar sabbin matakai tun 2024 domin dawo da haɓakar harkar.

Ya ce yanzu akwai mutane da dama da suka koma noman auduga, sannan ana samun sababbin masana’antu da ke tasowa, ciki har da wani kamfani da aka kafa kwanan nan domin samar da man angurya.

Ya ce man angurya na kasancewa cikin auduga, kuma ƙasashe da dama ciki har da Saudiyya suna buƙatar shi saboda inganci da rashin cutarwa ga lafiyar jama’a.

Dakta Buhari ya ƙara da cewa gwamnatin Zamfara ta himmatu wajen farfaɗo da tsofaffin masaƙu da suka daɗe a rufe domin samar da ayyukan yi ga matasa da inganta tattalin arziƙin jama’a.

A cewarsa, cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar ta ci moriyar tallafin kuɗi tun lokacin da Gwamna Lawan Dare ya hau mulki. Ya ce an bai wa ’yan kasuwa tallafi iri-iri, ciki har da na kyauta da kuma basussuka da ake shirin sakin su nan kusa.

Ya ce Zamfara ta shahara wajen noma da kuma arziƙin ma’adinai, kuma a baje kolin duniya sun gabatar da nau’ikan kayayyaki daga kowace Karamar Hukuma da nufin nuna abin da jihar ke da shi.

Ya ce akwai ma’adinai masu inganci a Zamfara, irin su zinare, granite da zinc, waɗanda suke jan hankalin masu zuba jari daga cikin gida da wajen ƙasar nan.

A cewarsa, cibiyarsu na ci gaba da samar da hanyoyin jan hankalin masu zuba jari domin bunƙasa masana’antu, musamman ɓangaren zinare da sauran nau’ikan ma’adinai. Ya ce akwai ƙasashe da dama da ke neman irin ma’adanan Zamfara, kuma a bara ma sun kai wasu kayayyakin jihar zuwa ƙasashen waje domin nuna damar da Zamfara ke da ita.

Ya ce mahimmancin baje koli shi ne bai wa jama’a damar ganin kayayyaki da damarmaki da ake da su, tare da jan hankalin masu sha’awar kafa masana’antu su yi haɗin gwiwa wajen gina kasuwanci mai ɗorewa.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe