Daga Ibrahim Muhammad
“Marigayi Galadiman Kano mutum ne mai haƙuri, juriya da iya danne ɓacin ransa.”
Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kano, tsohon ƙaramin ministan gidaje, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar ta’aziiyya da ya kai ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas na rasuwar mahaifinsu Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
ATM Gwarzo ya ce sun zo yin ta’aziya ne na rashin uba, kaka, Galadiman Kano wanda an yi babban rashi, domin sun yi aiki da shi shekaru 14 da suka wuce a lokacin da yake mataimakin Gwamna lokacin Malam Ibrahim Shekarau.
Ya jaddada cewa mutum ne mai haƙuri sosai da juriya a kan abubuwa da yawa. “Sau da yawa ko da wani abu ya ɓata wa Galadima rai, amma sai ya haƙura ya kau da kai,” in ji shi.
Abdullahi Tijjani Gwarzo ya yi kira ga iyalai da ‘yan’uwa da al’ummar Kano su yi haƙurin wannan rashin da ya shafi Kano da Arewa da ma ƙasa gaba ɗaya, su kuma ‘ya’yansa su cigaba da haɗin kai a tsakaninsu.






