Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke yi ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kafa wata Hisbah mai zaman kanta a Kano.
Little ya bayyana wannan yunƙurin a matsayin barazana ga zaman lafiyar jihar, wanda a cewarsa, na iya haifar da rikice-rikice da kuma kawo rashin daidaito a tsarin tsaron al’umma.
Alhaji Ibrahim Al-Amin Little ya ce, a halin yanzu ma ya umurci lauyoyinsa da su aika wa masu wannan yunƙuri da takardar gargaɗi, tare da shawartarsu da su janye wannan niyya tasu nan take.
Ya ce, idan har suka ƙi bin wannan umarni, zai garzaya kotu domin dakatar da duk wani yunƙuri da ka iya haddasa rikici ko kawo tangarɗa ga tsarin doka da oda a jihar Kano.





