Daya Ibrahim Muhammad
An ƙaddamar da littafin tarihin Gwamnan mulkin soja na farko na jihar Kano, Alhaji Audu Baƙo mai suna GOVERNOR AUDU BAKO MAN OF WISDOM AND FORESIGHT, wanda Kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya Dogo Manya Dogo ya rubuta..
Taron an gudanar da shi ne a Kano da ya sami halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na jihar Kano da Jigawa wato tsohuwar jihar Kano da suka haɗa da mataimakin Gwamnan jihar Jigawa Ahmad Usman Gumel da Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci na jihar Kano Gwani Wada Sagagi, wanda ya wakilci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a yayin taron.
Babban mai ƙaddamar da littafin, Alhaji A. A. Rano, wanda ya sami wakilcin ɗan’uwansa Alhaji Wada A.A. Rano, ya ƙaddamar da sayen littafin guda 25 a kan ₦25,000,000, shi kuma ya sayi kwafi 10 a kan ₦500,000, jama’a da dama ne dai suka ƙaddamar da sayen littafin.
Ambasada Hajiya Zainab Audu Bako, ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Alhaji Audu Bako tsohon Gwamnan jihar Kano na farko ta shaida wa ‘yan jarida mutuƙar jin daɗi da farin cikinsu bisa rubuta littafin da ya ƙunshi irin halayyar mahaifinsu da suka yi aiki tare tsawon lokaci.
Ta yi nuni da cewa, ana ganin irin ayyuka da ya yi ana cewa Audu Bako ne ya yi, amma mutane ba su fahimci wane ne shi ba ganin shi marubucin littafin yana tare da shi ya san shi da irin tunanin shi, akwai abin da ya sani game da shi da al’umma ba su sani ba, shi ne ya wallafa littafin.
Ya ce duba da yadda yanzu shugabanci ke tafiya a ƙasar nan babu kishi, babu damuwa da tausayin talaka, ba gaskiya da amana, saɓanin a lokacin mahaifinsu sun yi aiki tuƙuru ba tare da taɓa haƙƙin al’umma ba don haka suna godiya ga Allah gaskiyar mahaifinsu ya daɗa bayyana, littafin zai zama izina ga masu mulki da matasa masu tasowa su karanta su fahimci yadda ya yi kyakkyawan shugabanci domin a gyara lamarin.
Ambasada Hajiya Zainab Audu Bako ta ce suna jin daɗin idan ana faɗar ayyukan alheri da mahaifinsu ya yi da alfahari da shi suna roƙon Allah ya sa dubi sawunsa wajen aikata ayyuka nagari, ya tsare su da duk wani abu na ba daidai ba. “Mun gode wa Allah da Mahaifinmu da mahaifiyarmu suka bar mana baya mai kyau, wanda har gobe ana faɗar magana mai daɗi a kansu, sun kafa tarihin abin da ke amfanar da al’umma,” ta bayyana.
Ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf a kan ta taimaka ta ƙarasa mallaka masu sauran kadarorin Mahaifinsu da aka amince a mayar musu wanda a baya bayan juyin mulki da aka yi a ƙasar nan an karɓe kayayyaki na masu mulki bisa zargin na almundaha ne, amma daga baya aka wanke su gwamnatin Babangida ta ce a mayar wa kowa kayansa.
Ta ƙara da cewa sai dai su iyalan Audu Baƙo tana jin su ne kawai, har yanzu gwamnatin Kano da ta Jigawa ba su gama dawo musu da kayan ba, yawanci waɗanda abin ya shafa da yake suna raye sun karɓi nasu an wuce wurin, amma su har yanzu akwai wurare da dama da ba a dawo musu da su ba. “Don haka muna roƙo a dawo mana da su domin a raba mana gadonmu don sauke wa mamacin nauyi a makwanci kamar yadda malamai suka ce sai an saukewa mamaci bashi da raba gado,” ta ce.
Ambasada Hajiya Zainab Audu Bako ta jaddada roƙo tare da kokawa Gwamnan jihar Kano Injniya Abba Gida-Gida ya san maganar saboda haka don Allah ya kirawo lamarin duk wani abu da ya rage a hannun gwamnati na Mahaifinsu ya sakar wa iyalansa da sauke masa duk wani nauyi.
Shi ma marubucin littafin, Kwamishina ‘yan sanda mai ritaya CP. Manya Dogo ya bayyana cewa ya rubuta littafin ne bisa lura da ya yi mutane ba su fahimci wane ne Audu Baƙo ba, shekaru da ya yi na Gwamnan jihar Kano ba ya barci, ba ya hutawa, saboda aiki tuƙuru, amma sai aka zo aka wofintar da shi.
Ya ce suna tare da Audu Baƙo tsawon lokaci shekara 10 dare da rana ya san abubuwa da yawa a kansa irin ayyuka da ya yi a Kano babu wani Gwamna da ya yi kamarsa, amma sai ya ga ba a fahimce shi ba, abin ya dame shi sosai sannan mutane ba su sani ba Audu Baƙo yana da alaƙa da Kano, Mahaifiyarsa ‘yar Mariri ce Mahaifinsa ne ba daga Kano ba.
Ya ce, amma duk da yadda ya kawo cigaban Kano sai ya lura daga baya ba a yabawa abin da ya yi, ba a fahimce shi ba. “Audu Baƙo fa a cikin ɗan lokaci da ba wani kuɗi mai yawa ba ya yi damadamai masu yawa a Kano ɗaya daga ciki ma shi ne dam na biyu mafi girma a ƙasar nan kuma shi ba azzalumi ba ne.
Manya Dogo ya ce abin da Audu Baƙo ya yi a zamanin mulkinsa a gabansa a kan idonsa ya yi, amma a ƙarshe bai ga an fahimcice shi ko an yaba masa ba, don haka ya ce bari ya rubuta littafin ya shaida wa duniya ga yadda yake ga shi nan a rubuce mutane na yanzu da masu zuwa gaba su san me ya yi a Kano shi ya sa ya rubuta.






