Kabilar Baburawa Na Da Kyakkyawar Dangantaka Ta Zamantakewa Da Al’ummar Kano -Hassan Aliyu Shafa Sarkin Matasa

Daga Ibrahim Muhammad

Akwai dangantaka da alaƙa mai ƙarfi sosai tsakanin ƙabilar Baburawa da Hausawa jihar Kano da wasu kabilu ma daban-daban da suke tare da su.

Alhaji Hasan Aliyu Shafa Sarkin matasan jihar Kano na Baburawa ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce su da suke matasa suna tare da matasa na hausawa cikin zamantakewa mai aminci, kamar yadda su ma suka taso suka ga iyayensu suna zaune lafiya da yin auratayya a tsakani, yanzu a halin da ake ciki ma Baburawa a jihar Kano sun zama Hausawa saboda sun aura daga Hausawa su ma sun aura daga Baburawa wasu da dama ba sa jin harshen Baburawa sai Hausa.

Sarkin matasan jihar Kano na Baburawa Alhaji Hassan Aliyu ya ce a matsayinsu na matasa suna iya ƙoƙarin ƙarfafa matasan Baburawa da na Hausawa har ma sauran ƙabilu da aka tare kamar Marghi da Chibok Dakarkari da ma kowane yare da ya kusance shi gwiwa ta tallafa musu wajen sama musu ayyukan a wurare daban-daban a kamfanoni kama daga tuƙin mota, kanikanci da walda da sauran sana’o’i na hannu da kuma ganin sun nemi ilimi kuma ana samun nasara a kai.

Alhaji Hassan Aliyu Shafa ya bayyana gamsuwa da irin ayyuka da gwamnatin jihar Kano take a fannoni da dama na cigaban rayuwar al’umma ta na fitar da su kunya na irin gudunmawar da suka ba ta a yayin zaɓe, domin Baburawa sun ba da gudunmawa 100 bisa 100 domin tabbatar da nasarar Kwankwasiyya, kuma tabbas Gwamna Abba Kabir Yusuf yana iya ƙoƙarinsa wajen gudanar da ayyuka.

Ya ce a matsayinsu na Baburawa da suka fi kowace ƙabila da ke zaune a jihar Kano yawa, in aka ɗauke Hausawa ‘yan gari, sun haifa sun yi jikoki, sun zama ‘yan asalin Kano ko shi duk da ba a Kano aka haife shi ba, amma ya fi wayo a Kano fiye da garinsu, tun yana shekara 18 ya ke a Kano kusan yanzu ya shafe shekaru 37 a Kano.

Alhaji Hassan Aliyu Shafa ya ce in aka yi duba da yawansu, amma har yanzu ba su da wani da yake da muƙami a gwamnatin jihar Kano daga ɗan asalin ƙabilar Baburawa, wanda sune na biyu a yawa a Kano, kuma suna ba da gudunmawa cikkiya ga wannan gwamnati. Don haka suna fata Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na Jagora mai adalci su ma zai waiwayi ƙabilar Baburawa a ba su matsayi a gwamnatinsa.

Sarkin matasan jihar Kano na Baburawa ya ce yanzu haka ma suna gudanar da shirye-shirye na yin gagarumin taron buki nan ba da dadewa ba na nuna al’adun Baburawa a nan jihar Kano, wanda ‘yan ƙabilar za su halarta daga ciki da wajen jihar Kano da wajen ƙasar nan, suna fatan neman tallafin gwamnatin Kano da jami’an tsaro domin gudanar da taron cikin kwanciyar hankali.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe